Wata mata ‘yar aiki mai suna Happiness Dauda ta kubuta dakyar daga ukubar uwargijiyarta a Abuja bisa zargin ta dauke mata wayar salula.
Tun daga ranar da suka samu sabani kan haka, wato bayan wanda take wa aiki ta zargeta da sace mata wayar Salula a dakainta a lokacin da ta shiga yi mata share-share da goge-goge.
Tun daga wannan rana ta rika azabtar da ita, wahalar yau daban da na gobe.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=PJRJEN8crDo&w=560&h=315]