BIDIYO: Yadda direban adaidaita ‘Keke Napep’ ya dambace da jami’an Hukumar kiyaye Hadura, FRSC

0

Wani direban adaidaita ya dambace da wasu jami’an hukumar kiyaye Haddura ta kasa saboda sun kama a daidai yana aikin tukin sa.

Direban ya dare kan motan ma’aikata ya auna ya ce ya zai sauka ba. Daga karshe sai ya tube kayan jikin sa karkaf ya daka tsalle ya cakumi daya daga cikin jami’ai a garin Sapele jihar Benin.

Sannan kuma ya rika soka mishi naushi, yana cewa ku kashe shi, gani.

Sauran abokan ma’aikacin suka taru akan wannan mutum suka rika sharara masa mari suna naushin shi.

Shi ko dan adaidaita ya koma ya rungume motar jami’an yaki saki.

Share.

game da Author