Ban bijire wa umarnin Shugaban Kasa ba da na dakatar da shugabannin NSITF – Minista Ngige

0

Ministan Kwadago Chris Ngige, ya shaida wa Kwamitin Bincike na Majalisar Tarayya cewa dakatar da wasu shugabanni da manyan jami’an Hukumar NSITF da ya yi, bisa umarnin Shugaban Kasa ne, bai karya umarnin ba.

Ngige ya bayyana haka cikin amsar da ya bai wa kwamiti mai binciken ko an dakatar da shugabannin hukumar da wasu jami’ai ba bisa yadda doka ta gindaya ba.

Ranar 2 Ga Yuli ne Minista Ngige ya dakatar da Shugaban NSITF Adebayo Somefun da wasu manyan jami’an hukumar, bisa zargin kacaccala naira bilyan 3.4 a aikin horarwar da ba a gudanar ba kwata-kwata.

Dakatarwar ta zo ne wata daya bayan Sakataren Gwamnatin Tarayya ya raba wa Ministoci wasikar umarni daga Shugaban Kasa cewa, ministoci su daina saukewa, kora ko daaktar da shugabannin hukumomin da suke karkashin ma’aikatun su.

‘Ban Tafka Kuskure Ba’

Ngige a cikin sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES, a ranar Laraba, ya ce bai karya ka’ida, doka ko umarnin Shugaban Kasa ba.

Sanarwar wacce kakakin sa Charles Akpan ya ce Ngige ya bi tsarin da Dokar Kafa NSITF ta gindaya.

Ya ce dakatarwar ta taso ne bisa zargin kasa tantance sani ko ganin abin da aka yi da zunzurutun kudade har naira bilyan 3.4.

Ya kara da cewa masu binciken kudi ne suka yi filla-,filla da bayanan Kudaden da NSITF ta kashe daga 2013 zuwa 2018, Kuma suka gano tabbas an rika karya ka’ida wajen bayar da kwangiloli.

Ya ce an samu shugaban hukumar wanda ya sauka da laifi da kuma wanda ya maye gurbin sa, wato wanda aka dakatar.

Ya ce sauran wadanda aka dakatar din su ne masu mukaman manajojin da ke kula da bangarori daban-daban da su ma ake zargi da hannu a cikin harkallar.

“A matsayi na na Minista mai kula da hukumar NSITF, ba na bukatar tsayawa jira har sai an rubuto min takardar korafi, sannan na dakatar da wadanda bincike ya nuna sun yi badakala, harkalla da burum-burum da kudaden hukumar da ke karkashin Ma’aikata ta.” Cewar Ngige.

Ya ce dakatarwar “ai ba kora ba ce, amma dai mataki ne aka fara dauka da ka it’s kai ga zangon ladabtarwa.”

Share.

game da Author