• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Crisis in Jos

    BAUCHI: Matasa sun babbake gidaje da shaguna da dama a Warji bayan Rhoda Jatau ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW

    GUDUN YIN BIYU-BABU: Gwamnan Bauchi ya sayi fam ɗin sake yin takarar gwamna, daidai lokacin da ya fito takarar shugaban ƙasa a PDP

    Farin jinin Buhari da mara min baya da yayi ya sa na samu daukaka a siyasa – Bala Mohammed

    Kano State Assembly

    Dan majalisar dokoki na jihar Kano ya doka ‘Ribas’ bayan ya tsunduma lambun jam’iyyar NNPP, ya ya rungumi tsintsiyar sa ya dawo APC

    Yadda EFCC ta damke Akanta Janar din Najeriya bisa zargin harkallar naira biliyan 80

    Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Akanta Janar ɗin da ake zargi da kantara satar naira biliyan 80

    Nigerian Pilgrims

    HAJJIN BANA: Duk wanda ya zarce shekaru 65 bashi ba Hajji bana – Hukumar Alhazai

    Beggars

    Almajirai da mabarata sun kwararo Abuja – Mahukunta

    HARƘALLAR KWANGILA: EFCC ta kama Patricia Etteh, tsohuwar Kakakin Majalisar Tarayya

    Ƴan bindiga sun ƙona hedikwatar karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra

    UMARNIN SALLAMA DA KUJERAR MINISTA: Pauline Tallen, Timiprr Sylva duk sun janye daga takara

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

BAKIN HADARI DAGA GABAS: Yadda Gogarman Ta’addanci Shekau ya mamaye Gabas, ya darkake yamma, ya dabaibaye tsakiyar Najeriya

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
July 13, 2020
in Babban Labari, Rahotanni
0
Abubakar Shekau

Abubakar Shekau

Abubakar Shekau, gogarman ‘yan ta’addar Boko Haram da aka rika yi wa kallon raini, ana ganin wa wani saida-kaji-saida-kaji, sai ga shi an yi sake ko sakaci, ya zama gawurtaccen gogarman da ke kokarin sayar da Arewacin Najeriya rankatakaf din ta.

Nazari ya tabbatar da wata shiryayyar ajandar da Shekau da mabiyan sa ‘yan Boko Haram ke kitsawa domin karasa mamaye Yankin Arewa maso Gabas, su darkake Arewa maso Yamma, ku su dabaibaye Arewa ta Tsakiya.

Sabon Shirin Shekau Na Mamaye Arewa Kakaf:

A yanzu Shekau ya dawo ya na kulla kasancen sasantawa da juna tsakanin sa da wadanda ya rika kafirtawa da suka balle, suka raba hanya.

Sannan kuma ya rage zafi da rakadin tsatstsauran ra’ayin saurin kafirtawa da ya ke yi. Ya kuma shata rawar da malaman cikin tafiyar za su rika takawa da matsayin zarata, dakaru da baraden-mutuwa-dole ke takawa a tawaga da eundunonin sa.

Ta kai a yanzu Shekau ya tashi tsaye ya na kokarin kafa kasaitacciyar daukar ‘Halifan Juhadin Afrika’ a karkashin ikon sa.

Ya yi yunkurowar da bai taba yin irin ta ba, tun bayan raba hanyar da ya yi da Al Qaeda cikin 2013.

Ba kamar yadda aka rika yi masa kallon wani galhanga ko wani garangaudiyar dan daban da ke shirme a bidiyo ya na harba bindiga a sama a cikin bidiyo ko cika-baki ba, a yanzu Shekau ya zama wani gogan tsara dabarun yadda zai kai gaci ko tsallake siradi da tarko.

Masana tsiyar yakin sunkuru a Maiduguri da Abuja sun hakkake cewa ba a taba samun gogarman dan ta’addar da ya addabi wani yanki a cikin shekaru 10, har ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 30,000, sama da milyan 2 suka rasa gidajen su, kamar Shekau ba.

Tun bayan mutuwar Muhammad Yusuf cikin 2009, bayan Shekau ya hau ‘halifanci’, ya tsallake yunkurin juyin mulki da aka nemi yi masa ba sau daya ba – musamman har daga bangaren da ya fi shi kayan fama nesa ba kusa ba.

A yanzu Shekau ya zauna daram a kan kujerar sa, sai ma kokarin kara fadada ‘daular sa’ ya ke ta yi.

Sauya fasali da akalar jagorancin da Shekau ya yi, ta faro ne tun bayan zaman sa a Kano cikin 2012, zuwa hijirar da ya yi zuwa dajin Alagarno da Sambisa a Barno.

HumAngle ta gano cewa bayan Shekau ya rika shekar da jinainan daruruwan mabiyan sa saboda tankiyar da ba ta taka kara ta karya ba, sai gogarman ya gano cewa wannan danyen hukunci da ya ke yankewa ya janyo zaratan sa na ballewa daga gare shi su na arcewa cikin kasashen duniya. Har ma wasu na komawa bangaren Ansaru cikin 2012 da ISWAP cikin 2016.

Masu masaniyar lamurran da ke kai-kawo a Boko Haram, kamar yadda HumAngle ta ruwaito, sun nuna cewa sun fara fahimtar Shekau ya fara rage zafin akida, sai kuma sasautawa zafin da ya kan nuna kan kwamandojin sa. An hakkake a yanzu ya na ta kokarin sasantawa da mayakan sa da suka kauce daga wajen sa suka fandare masa.

“Sai dai kuma har yanzu an hakkake cewa ba ya ga-maciji shi da ISWAP.”

Gamin-gambizar Shekau Da ‘Yan-rugumutsi, Sa’alaba Da Bakura A Tabkin Chadi:

Yadda Shekau ke kara fadada yankunan da ke hannun sa a Yankin Tafkin Chadi, ya nuna irin hangen nesan da ya ke yi da muradin sa na kafa daular ‘halifanci’. Ga shi kuma har yau tabaran-hangen-nesan jami’an tsaro ya kasa hango tungar da Shekau ya yi tunga ko mashekari.

A Yankin Tafkin Chadi, Shekau ya kwantar da kai ya ja hatsabibin gogarma Sa’alaba da tantirin dan dadi-mutuwa, Bakura. Wadannan wasu rikakkun mayaka ne da suka ki mara was kowane bangare baya, yayin da aka samu sabani tsakanin Abu Mus’ab dan Mohammed Yusuf da Mamman Nur, wanda rundunar sa ta ISWAP ta taba kece raini a da Boko Haram din Shekau cikin 2016.

Ganin yadda ‘yan ta’addar rundunar Sa’alaba/Bakura su sama da 300 suka hade a karkashin Shekau cikin Disamban 2018, ya sa a farkon 2019 ikon Yankin Tafkin Chadi mai arziki ya zama hannun bangarorin Shekau da da ISWAP.

Yadda Shekau ke kulla siyasar diflomasiyyar kulla yarjejeniyar zumunci tsakanin sa da kananan kungiyoyin ‘yan ta’addar da ke waje gefen Sambisa da Kudancin Barno wasu sassan Kamaru, ya na ba su iko/’yancin kai na su haren-haren daban, wannan na nuna irin mamayar da wannan kulla zumuci ya yi a kokarin da Shekau ke yi zama Babban Kwamanda baki daya kuma ‘halifan daukar’ da ya ke neman kafawa.

Tuni Shekau ke ta kokarin sake dinke baraka tsakanin sa da mayakan da suka balle, Amma kuma suka ki Mika wuya ga tayin afuwar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi musu.

Wannan kuwa kamar wata karin magana ce da ake yi wa kazami, wai ‘dauda karin karfi wanda bai sani ba ka wanka.’

Hakan kuwa na kara wa Shekau karfi, kamar yadda wani tubabben dan Boko Haram ya bayyana wa HumAngle cewa bayan ya tsere daga Dajin Sambisa, cikin 2018, ta koma Kano, ya kasa samun aiki.

Irin haka ta masu wasu zaratan Boko Haram da dama sun kasa samun wurin zama a cikin al’ummar su a Arewacin Najeriya.

Kullum suna jin tsoron haduwa da wani dan Maiduguri da san su. Rayuwa ta zame musu jangwam.

“Wasu sun koma sun shiga Ansaru, sun darkaki Arewa maso Yama, saboda sun kasa samun aiki ko madogara a cikin garuruwa.” Inji tsohon dan ta’addar.

“Amma yanzu tunda Shekau ya fadada ‘daular’ sa har Zamfara, ka ga kenan za mu iya komawa can mu mike kafar mu ba tare da tsoron komai ba.”

Majiya ta shaida wa HumAngle a ranar 16 Ga Yuni kamar yadda ta ruwaito cewa Shekau na ta kokarin kula zumunta da mayaka a Tadaba, Kogi, Katsina da Sokoto.

Sai dai ba a sani ba ko Gwamnatin Najeriya da sauran kasahen da ke yaki da Boko Haram na bibiyar wannan shiri da kulle-kullen fadada yankunan da Boko Haram ke ta kokarin yi.

Tags: Abu Mus'abAbujaBoko HaramHausaHumAngleIPSWAPLabaraiNajeriyaNewsPREMIUM TIMESShekau
Previous Post

Minista Akpabio ne ya fara kafa garken masu satar kudin NDDC -Tsohuwar Shugabar NDDC

Next Post

Yadda na sharara wa minista Akpabio mari da ya nemi afka min – Tsohuwar shugabar NDDC

Yadda na sharara wa minista Akpabio mari da ya nemi afka min - Tsohuwar shugabar NDDC

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • BAUCHI: Matasa sun babbake gidaje da shaguna da dama a Warji bayan Rhoda Jatau ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW
  • FALLASA: An bankaɗo ɓoyayyar asusun ajiya na Jeremiah Useni a tsibirin Jersey wanda ya kimshe biliyoyin naira a lokacin yana ministan Abuja
  • RAHOTON MUSAMMA: Yadda Rigima ta ɓarke tsakanin Tambuwal da Hukumar WAEC kan kuɗin jarabawar ɗalibai
  • Farin jinin Buhari da mara min baya da yayi ya sa na samu daukaka a siyasa – Bala Mohammed
  • Gwamnatin Tarayya ta fara raba wa fakirai da talakawan jihar Kebbi tallafin kudade

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.