Gwamnatin Kano ta bayyana cewa a bana ba za ayi bukukuwan da aka saba yi ba a lokacin bukin sallah.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Mohammed Garba ya bayyana haka bayan taron kwamitin zartaswar jihar da aka yi ranar Laraba.
” Kwamitin ya amince cewa ba za ayi hawan Sallah dana al’ada da aka saba ba a jihar ba sannan kuma gwamnati za ta tabbata kowa bi doka da oda wajen kiyaye sharuddan dokokin hukumar NCDC, wato na kariya daga Korona.
” Jami’an gwamnati zasu sa ido domin tabbatar da kowa ya bi doka da oda a wajen sallar Idi da za a yi.
” Sannan kuma gwamnati ta amince duka sarakunan jihar za su tafi masallaci idi a motocin sune ba dawakai ba.
” Bayan haka gwamnati za ta taimakawa mutane da takunkumin fuska, da man tsaftace hannaye.
A karshe Garba ya ce gwamnati ta yi haka ne domin kada a maida hannun agogo baya game da nasarorin da gwamnati ta samu a jihar na dakike yaduwar Korona.
Ana sa ran za a yi Idi ranar 31 ga Yuli.