Hukumar Hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa babu abinda ya hada cutar Korona da zazzabin cizon sauro.
Hukumar ta ce kwayoyin cututtukan dake haddasa cutar covid-19 ba shine ke kawo zazzabin cizon sauro ba.
Masana kimiyya sun bayyana cewa kwayoyin cutar SARS-CoV ne ke kawo cutar covid-19, sauro kuma ke kawo zazzabin maleriya.
Alamun cutar covid-19 sun hada da rashin iya numfashi yadda ya kamata, zazzabi, ciwon makogoro, tari ko atishawa, yawan jin kasala a jiki, rashin iya jin dandano abinci da kamshi, gudawa, mura da sauran su.
Shi kuma alamun zazzabin cizon sauro sun hada da ciwon Kai, yawan yin zufa, ciwon gabobbin jiki, amai, suma, yawan Jin kasala da kuma masassara.
NCDC ta yi kira ga mutane da su kiyaye shan magani ba tare da izinin likita ba sannan su gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da Suka ji ba daidai ba a jikinsu.
Sakamakon gwajin cutar coronavirus da NCDC ta first ranar Litini ya nuna cewa an Sami Karin Mutum 563 da suka kamu da cutar a Najeriya.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –100, FCT-102, Filato-52, Kwara-50, Abia-47, Kaduna-35, Benue-34, Oyo-26, Ebonyi-24, Kano-16, Niger-15, Anambra-14, Gombe-12, Edo-11, Rivers-6, Nasarawa-5, Delta-5, Borno-3, Enugu- 2, Bauchi-2 da Kebbi- 1.
Yanzu mutum 37,225 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 15333 sun warke, 801 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 21,091 ke dauke da cutar a Najeriya.
Discussion about this post