Gwamantin Tarayya ta bada da ranakun Alhamis 30 ga Yuli da ranar Juma’a, 31 ga Yuli ranakun hutun Babbar Sallah.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne bayyana haka haka ranar Talata, a madadin gwamnatin tarayya, inda ya ke taya daukacin Musulmi da ‘yan Najeriya murnar zagayowar ranar babban salla na shekarar 2020.
Aregbesola ya kuma roki ‘yan Najeriya su hada hannu da gwamnatin Muhammadu Buhari, domin a samu nasarar daga Najeriya zuwa kololuwa can sama a wajen gyara kasa Najeriya.
Ya kuma yi kira ga ‘Yan Najeriya su kiyaye dokoki da sharudan gujewa kamuwa da cutar covid-19 da gwamnati da hukumar NCDC ta bada a lokacin shagulgulan sallah.
Ana sa ran za a yi sallar Idi ranar Juma’a.
Discussion about this post