BABBAN SALLAH: Matawalle ya raba raguna 5000, shanu 993 a Zamfara

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya raba raguna 5000 ga mutanen jihar sa domin layya na babban sallar.

Baya ga raguna 5000, Matawalle ya raba wa al’ummar jihar jibga-jibgan shanu sama 993.

Darekta Janar na hukumar wayar da kan mutane na jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya bayyana haka da yake zantawa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

” Mu a jihar Zamfara Gwamna Matawalle ya baya wasa da taimakawa marasa karfi. Hakan na daga cikin abin da ya sa a gaba. Idan ba a manta ba a lokacin karamin sallah ya taimaka wa marasa karfi sama da mutum 100,000 da kayan sallah, abinci da kayan masarufi.

” Haka kuma ko a shirin babban sallah da ake ciki yanzu gwamna Matawalle ya raba, kayan abinci ga kungiyoyi, kayan sawa baya ga raguna da Shanu da ya rarraba.

A Karshe Idris ya ce wadanda za su amfana da wannan tallafi sun hada da ma’aikatan gwamnati, Kungiyoyi, matalauta da dai sauransu.

Share.

game da Author