Sufeto Janr din ‘ Yan sanda Mohammed Adamu ya bayyana cewa babu ruwan ‘yan sanda da tsare dakataccen shugaban riko na hukumar EFCC, Ibrahim Magu.
Idan ba a manta daya daga cikin Lauyoyin Magu dake tsare a wani gini mallakar, ‘Yan sandan Najeriya, ya rubuta wa sufeto Janar Adamu shimfidaddiyar wasikar neman a bada belin Magu.
Lauya Tosin Ojaomo, shaida cewa a shirye yake da su cika duk sharuddan da za a gindaya musu wajen bada belin Magu din.
Sai dai kuma bayan wannan wasika ta isa ga sufeto Adamu, sai ya aika masa da amsa yana mai cewa ” Babu abinda ya hada ‘yan sanda da tsare Magu.” Mai neman beli ya gaggauta tuntubar kwamitin dake binciken Magu karkashin Mai shari’a Ayo Salami domin sanin wanda ke tsare da shi.
Har yanzu dai ana cigaba da tuhumar Magu bisa wasu harkalla da ake zargin sa da hannu dumu-dumu a ciki, wanda har yanzu kwamitin dake bincikar sa basu bankado laifi koda daya bane da aka tabbatar ya aikata na almundahana, cin hanci ko rashahawa.
A ranar Laraba, shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da sakataren hukumar, da wasu manyan darektocin hukumar dake hedikwatar ta a Abuja,da wasu daga cikin shugabannin hukumar na shiyoyyin kasar nan.
Idan ba a manta ba sai da Magu ya fito aiki daga ofis zai tafi hedikwatar ‘yan sanda sai wasu jami’an tsaro suma datse masa hanya suka yi awon gaba dashi.
Tun daga wannan rana yake tsare, sai dai da safe azo a garzaya dashi fadar shugaban kasa domin amsa tambayoyin kwamiti.
Discussion about this post