Hukumar EFCC ta bayyana cewa ba a kama shugaban ta Ibrahim Magu ba kamar yadda a ke ta yadawa. Hukumar ta ce da kan sa ya kai kan sa fadar shugaban kasa bayan an mika masa takardar gayyata zuwa fadar gwamnati.
An gayyaci Magu fadar shugaban kasa domin ya bayyana a gaban wani Kwamitin binciken bisa wasu zargi da ake masa.
Ita ma hukumar tsaro na SSS ta bayyana cewa ba ita bace ta damke Magu kamar yadda wasu jaridun suka ruwaito.
Karanta labarin mu na baya
Jami’an tsaro sun yi wa Karamin Ofishin EFCC da ke Wuse II kawanya, su ka damke Shugaban EFCC din na Riko, Ibrahim Magu.
An yi awon gaba da shi da rana, bayan jami’an tsaron sun kwashe minti 30 su na tankiya da jami’an tsaron Magu.
Sun dai hana masu tsaron Magu bin su, domin su ga inda aka nufa da shi.
An garzaya da shi cikin Fadar Shugaban Kasa, domin amsa tambayoyi daga kwamitin binciken da Shugaban Kasa ya kafa, domin binciken zargin da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi masa.
Malami dai ya zargi Magu da yi wa shirin yaki da rashawa kafar-ungulu da kuma yi wa wasu kudaden da Hukumar EFCC ta kwato, irin abin nan da Hausawa ke kira ‘sata-ta-saci,-sata.’
Majiya daga EFCC ta ce tuni har lauyan EFCC Rotimi Jacobs ya garzaya Fadar Shugaban Kasa inda Magu ya ke a yanzu.
Ko EFCC ko SSS babu wanda ya ce komai dangane da kamun da aka yi wa Magu.
Jami’an Yada Labaran su ma da aka kira, kin cewa komai suka yi.