Ministan kwadago ya roki kwamitin majalisa da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal da su yi hakuri bisa cecekucen da ya barke tsakanin ‘yan kwamitin majalisar da karamin ministan kwadago, Festus Keyamo a makon da ya gabata.
Ngige ya bayyana a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.
Ngige ya roki ‘yan majalisar, ya kuma ce irin haka ba zai sake aukuwa ba.
Idan ba a manta ba, Karamin ministan Kwadago Festus Keyamo ya fallasa cewa cikin ma’aikata 774,000 da gwamnatin tarayya zata dauka domin rage radadin talauci da yayi wa matasan Najeriya katutu, majalisar kasa kawai ta zaftare kashi 15% na wadanda za a dauka, wanda yayi daidai da akalla mutum 116,100.
Minista Keyamo ya bayyana haka da yake halartar taron kwamitin majalisar domin tattauna yadda za a raba ayyukan da kuma inda aka kwana.
Abin dai bata wanye da dadi ba domin ana cikin taron a ka barke da jefa wa juna zafafan kalamai.
Sanatoci da mambobi na son a kori ‘yan jarida daga dakin wannan ganawa, shi kuma minista Keyamo na cewa ba za a kore su idan gaskiya ake so a yi.
Majalisar kasa ta ware naira biliyan 54 domin daukan matasa aiki a kowacce karamar hukumar kasar nan. Za adauki akalla mutum 1000 daga kowacce karamar hukuma.
Amma kuma duk da mutum sama da 100,000 da ‘yan majalisan suka tilasta a basu, har yanzu sun yi babakere suna su a danka musu komai, su wawushe gaba daya, ‘yan Najeriya kuma ko oho.
A haka cikin rudani qldai aka watse daga wannan taro baya Keyamo ya nemi ya kwance musu zani a kasuwa.
Shugaba Muhammadu Buhari yayi alƙawarin fidda ‘yan Najeriya sama da miliyan 100 daga kangin talauci a dan kankanin lokaci.
Hakan yasa ana ta kirkiro shirye-shirye da zai samar da haka a kasa Najeriya.