Wani hasalalle Mai nemar wa ‘yan Najeriya hakki, ya maka dukkan jiga-jigan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da suka raka gawar Abba Kyari makabarta.
Kyari, wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, an binne gawar sa a Makabartar Gudu da ke Abuja, a ranar 18 Ga Afrilu, bayan ya mutu sanadiyyar cutar Coronavirus.
Mai kara Tope Akinyade, ya maka su Kutun Majistare da ke Kado, Abuja, inda ya nemi kotu ta hukunta su, saboda sun karya dokar killace mutane a gida da gwamnatin tarayya ta kakaba a lokacin.
Ya ce akwai rashin adalci matuka ga ‘yan Najeriya wadanda aka rika kamawa ana hukuntawa a lokacin zaman gida tilas, amma kuma ga wasu gungun jama’a sun karya dokar, babu wanda aka hukunta daga cikin su.
Ya ce idan dai har gwamnatin Buhari adalci ta ke kururuwar tabbatarwa, to bai ga dalilin da zai sa a rika bin talakawa ana kamawa idan sun karya dokar Korona ba. Su kuma wasu gungun na jikin gwamnati sun karya dokar amma an kyale su.
Daga cikin wadanda Tope ya maka kotu, akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Ministan Sufurin Jirage, Hadi Sirika, Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Ministar Harkokin Agaji da Jinkai, Sadiya Umar.
Akwai kuma Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu, jami’in yada labarai na soshiyal midiya, Bashir Ahmed, Mashawarcin Shugaba Buhari kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu da wasu jiga-jigan gwamnatin masu yawa.
Mai Shari’a Celestine Odo ya nemi ya nuna cewa Mai shigar da kara ya yi kuskure tunda wadanda ake kara din ba su sa hannu a takardar kasar su da ya yi ba.
Sai dai kuma shi Tope ya tunatar wa Mai Shari’a din cewa shi fa kai tsaye ya kawo kara a kotu, bai yi wani biye-biye ta hannun ‘yan sanda ba.
Ya ce aikin alkali ne ya aika wa dukkanin wadanda ake karar sammacin da za su sa hannu. Domin shi dai ya yi abin da dokar Najeriya ta ba shi ‘yancin yi wajen shigar da karar a kotu.
Mai Shari’a ya dage sauraren shigar da karar, ya ce a koma kotu ranar 4 Ga Agusta, domin ci gaba da saurare.