An Kama mutane ukun da Suka kashe likita a Abuja

0

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Abuja, ta damke wasu mutane uku da ake zargi da kashe wani likita da ya kware wajen hada magunguna.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan Abuja, Anjuguri Manzah ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranar Talata, a garin Abuja.

Manzah ya ce an kashe Sunday Ike wanda shine sakataren yada labarai na kungiyar masana hada magunguna reshen babban Birnin Tarayya, Abuja, ACPN ranar 19 ga watan Yuni a shagonsa da yake saida magani a Unguwar Gwarinpa a Abuja.

Ya ce Binciken da Suka gudanar ya taimaka wajen gano wayar salula Kirar Huawei da mota kirar Toyota Camry duk na mamacin da aka sace.

Manzah ya ce sun Kama Mutum biyu a Lafia jihar Nassarawa dayan Kuma garin Jos jihar Filato.

“Mun Kama Mutum biyu da motar mamacin a garin Lafia jihar Nassarawa sannan daya da wayar salular na mamacin a garin Jos Jihar Filato.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da binciken domin kamo shugaban kungiyar wadannan mahara.

Share.

game da Author