Jam’ian rundunar Sibul Difens a Kaduna sun damke wani limamin Cocin ,Faith Agape dake Unguwar Narayi, a Kaduna mai suna , Joseph Alhassan, bayan an zarge sa da yin lalata da ‘yar aikin sa na tsawon shekara 5.
Wannan yarinya dai wanda ‘yar asalin karamar hukumar Kagarko, tuni har iyayen ta sun tafi da ita bayan samun labarin abinda ya faru tsakanin ta da fasto Alhassan.
Shi ko Fasto Alhassan, wanda dan Asalin Karamar hukumar Lere ne, garin Saminaka ya karyata wannan zargi, inda ya ce shi kazafi aka yi masa amma abinda ake zargin sa da shi babu kamshin gaskiya a ciki.
Zargin Fasto Joseph Alhassan
Ma’aikatar jin dadin mutane na jihar Kaduna ce ta shigar da kara kotu tana tuhumar Fasto Alhasan bisa zargin yin lalata da ‘yar aikin da ke gidansa rukunin gidaje masu saukin kudi dake Shagari, Barnawa Kaduna.
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Bridge that Gap Initiative, ta kai karar haka ma’aikatar.
An samu bayanin cewa shekara biyar kenan wannan yarinya na aiki a gidan faston.
Fasto Alhassan yana nan tsare a hukumar Sibul Difens a Kaduna.