An bindige jami’in soja a Kogi, an sace wani sojan a Fatakwal

0

Wani jami’in soja da ke bataliya Sojojin Atilere ta 353, da ke Ojo a Lagos, ya gamu da ajalin sa, yayin da ‘yan bindiga suka bindige shi.

Haka PREMIUM TIMES ta tabbatar da afkuwar al’amarin.

Abubakar mai lambar shiga soja ta N/13600, ya fada a hannun ‘yan bindigar da suka yi shinge kan titin Okene zuwa Lokoja, hatsabibin titin da ya yi kaurin suna wajen garkuwa da matafiya da kuma bindige jama’a.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Abubakar ya baro Lagos ne kan hanyar sa ta zuwa Kwalejin Kananan Hafsoshi a Jaji, domin halartar kwas din kananan Hafsoshi.

An bindige shi lokacin da ya ke tafiya tare da matar sa da kuma mahaifiyar sa, a cikin motar sa kirar Honda.

An bude wa sojan wuta, sannan suka yi garkuwa da matar sa da kuma mahaifiyar sa.

Sauran jami’an sojojin da ke biye da shi a wata motar, sun auna arziki, inda kadan ya rage a harbe su. Suka kauce, suka tsere a sukwane.

Tuni aka dauki gawar sojan aka ajiye ta a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Lokoja. Sannan kuma aka fantsama neman matar sa da mahaifiyar sa.

Kwana daya kafin kisan Mohammed Abubakar, wasu mahara sun kame Laftanar M. Yohanna da ke Dibijin na 6 da Sojojin Najeriya da ke Fatakwal.

Majiya ta ce an yi garkuwa da ita bayan an kama shi a unguwar GRA, Fatakwal, kuma har yau ba a sake ganin sa ba.

Yohanna ta na da lambar soja N/18288F, kuma dan rukuni na 51 ne a jerin daliban NDA.

Wadanda ke kwas daya tare da ita, sun ce su na addu’a Allah ya kubutar da ita.

An kasa samun lambar kakakin sojojin Najeriya Sagir Musa, ballantana a ji karin haske daga gare shi.

Share.

game da Author