An bayyana dalilin da ya sa helikwafta dauke da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya yi hatsari a garin Kabba, Jihar Kogi.
Helikwaftan ya yi hatsarin ne a ranar 2 Ga Fabrairu a garin Kabba, dauke da Osinbajo da wasu mukarraban sa su takwas.
Shugaban Hukumar Bibiyar Hadurra ta Kasa (AIB), Akin Olateru, ya ce direban jirgin ne ya yi amfani da salon sauka wanda ba daidai ba ne ya yi amfani da shi.
Sannan kuma ya ce direban bai bi ka’idar da tsarin sauka kasa da jirgi mai saukar ungulu da kamfanin da ke da jirgin ya gindaya ba.
Jirgin mai lamba AW 139, samfurin Agusta Westland, ya yi saukar ungulu ne a cikin wani filin kwallo.
“Direban jirgin ya isa garin Kabba lokacin gari ya yi biji-,biji da hazo, shi kuma sai ya rika gani garara-gagara.
“Yayin da ya zo sauka, sai ya nufi filin kwallo a sukwane, tsananin sa filin da zai yi saukar-ungulu din ne.
“Bayan girgin ya karci kasa ya rargara kasa, ya tsaya bayan ya hantsila bangaren dama. Amma Mataimakin Buhari da sauran ‘yan rakiyar takwas, babu wanda ya ji ciwo a jikin sa.
Cikin wadanda ke tare da Osinbajo a cikin jirgin, har da Mashawarcin Buhari a Lamurran iyasa, Babafemi Ujudu.
Discussion about this post