Daya daga cikin makusancin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya rasu.
Marigayi Funtua ya rasu ranar litinin da dare.
Daya daga cikin iyalan sa ya shaida cewa marigayi Sama’ila Funtua yi rasuwar farad daya ne, domin ba wai yana kwance bane bashi da lafiya.
Shine mai kamfanin gine-gine na Bullet sannan fitaccen dan siyasa ne kuma mawallafin jarida.
Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da sakon ta’aziyyar sa ga iyalan marigayi Isma’ila Funtua.
” Ko da na samu labarin rasuwar marigayi Isma’ila Isa, na yi matukar jin rugugin rashin sa. Mutum ne da muke tare a tsawon gwagwarmayar siyasa ta.
Allah yaji kan sa amin.