Akeredolu bai ci zaben 2016 ba, mu muka shirya magudi ya yi nasara -Tsohon Sakataren Gwamnatin Ondo

0

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Ondo da ya ajiye aiki ranar Litinin, ya bayyana cewa Gwamnan Ekiti Rotimi Akeredolu bai ci zaben gwamna na 2016 ba, su ne dai suka dora shi da karfin magudi.

Sunday Abegunde, ya yi wannan kakkausan ikirari ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Radiyon Crest FM da ke Akure, Babban Birnin jihar Ondo.

Ya ce shi da wasu mutane ne wadanda bai ambaci sunayensu ba, suka yi magudin da ya kai Akeredolu gwamna a zaben 2016.

“Mu muka yi tuggu da magudin da mu ka yi, har Akeredolu ya ci zabe da magudi.

“Duk da haka, banda wahala babu abin da na sha a hannun sa. Bai rika fitar da kudaden da ofishi na ke bukata domin ayyukan da suka wajaba ba na tafiyar da ayyukan ofis da su ba.

“Har karya da ksrairayi ya rika kantara min, wai duk wata ya na ba ni naira milyan biyar. A gidan wa ya taba ba ni naira milyan biyar din?

“Na kai kukan abinda ya ke yi minga Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi. Ya yi alkawarin zai hada mu a Abuja mu sasanta junan mu. Na ce wa Fayemi idan Akeredolu ya kara cewa ya na ba ni naira milyan biyar, ko da rana daya ce, to zan tona masa asirin yadda ya ci zabe da kuma fallasa irin makudan kudaden da ya ke sata.”

Abegundu ya ce Akeredolu bai ci zabe ba, su ne suka yi magudin da suka dora shi kan mulki.

“Dama bai ci zabe ba, mu muka dora shi. A yanzu kuma mun gaji da yadda al’ummar mu ke shan wahala. Don haka a wanann zaben 2020 ba za mu goya masa baya ba.” Inji tsohon Sakataren Gwamnatin Ondo, wanda ya sauka daga mukamin sa, makonni kadan bayan Mataimakin Akeredolu mai suna Agbola Ajayi.

Share.

game da Author