Abin Da Kamar Wuya: Anya Barcelona za ta kai labari kuwa?

0

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Spain bata ji da dadi ba a hannun Athletico Madrid duk da an tashi wasa kunnen doki ne.

Barcelona na bukatar ta yi nasara a wannan wasa idan har tana so ta ja da Real Madrid wajen cin gasar lik din kasar Spain a wannan kakar kwallon kafar.

Barcelona sun tashi wasa da Athletico 2-2.

A dalilin wannan canjaras da Barcelona ta buga, Madrid na sama da ita da maki daya sannan ta na da kwantan wasa daya da za ta buga.

Idan ta yi nasara a wannan wasa za ta yi wa Barcelona nisa da maki hudu kenan a saman tebur.

Share.

game da Author