Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce dangane da wanda ake ganin za a nada domin ya gaji kujerar Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu.
Kwanakin Magu hudu kenan a tsare, ana yi masa tambayoyi dangane da zargin da Kwamitin Bincike na Shugaban Kasa, karkashin tsohon Cif Joji Ayo Salami ke yi masa.
Tun bayan dakatar da shi da aka yi, har yau ba a nada madadin sa ba. Shi ma kuma dama na riko ne har sama da shekaru hudu, tun bayan nada shi.
Yadda Ake Nada Shugaban EFCC:
Sashe na 2(3) na Dokar EFCC ta 2005, ya ce “Wanda ya fi saura matsayi a kasan Magu, kuma jami’in tsaron da ya shafe shekaru 15 a cikin harkar tsaro, shi za a nada ya rike ragamar EFCC.”
“Amma dokar ta bai wa Shugaban Kasa karfin ikon ya cire duk wani jami’in Hukumar da aka kama da laifin da ya dace a cire shi.”
“Idan an cire shugaban EFCC, to a nada wani daga mafi girman matsayi a mukarraban sa. Shi kuma zai karasa wa’adin da wanda aka cire ba karasa ba ne.”
“Idan za a nada sabo, ys kasance jami’in da ke kan aikin tsaro ne, ko kuma wanda ya yi ritaya. Kuma kada ya gaza kaiwa mukamin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (ASP), ko wani mai kama da wannan. Kuma ya kasance ya na da kwarewar aikin tsaro, akalla na shekaru 15.
*Shugaban Kasa zai iya cire shugaban EFCC a duk lokacin da ya aikata ba daidai ba. Ko aka same shi ya kasa gudanar da aikin da aka dora masa, ta dalilin nakasa ko rashin lafiyar da ta hana shi iya gudanar da aikin sa.”
Discussion about this post