Dan Uwa kuma babban aminin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Mamman Daura ya bayyana cewa salon mulki na karba-karba da ake yi a Najeriya ya zama tsohon yayi yanzu.
Mamman Daura ya ce Najeriya ta ‘rika ta yi kwarin’ da yanzu ta watsar da tsarin karba-karba a maida hankali wajen zabo wanda ya fi cancanta a 2023.
BBC Hausa ta wallafa hira da tayi da Mamman Daura wanda a ciki ne ya bayyana haka.
” Wannan tsari na karba-karba wajen zaben shugaba a Najeriya bai haifar da ‘da mai ido ba wanda aka fara tun a 1999.” Maimakon haka Daura ya ce a maida hankali wajen tsaida wanda ya cancanta ne ba sai an bi wannan tsari na karba-karba ba.
Sai dai kuma ‘yan kabilar Igbo, wato Inyamirai sun maida wa Daura martani bisa wannan kalamai na sa.
Sun ce sai da shi da dan uwansa shugaba Buhari suka kwankwadi romon mulki ta hanyar karba-karba sannan ne zai fito yanzu yace yana bada shawarar kada a bi haka a 2023.
” Shi kansa Buharin ba ya fi duka ‘yan Najeriya bane cancanta aka zabe shi, haka manyan hafsoshin tsaron kasar nan da suke zaune daram a kujerun su shekaru da dama ba a cire su ba, suma ay ba sun fi sauran iya aiki bane.
Martanin Inyamirai
Wata guguwar iskan siyasar shugabancin Najeriya ta kada a ranar Laraba, yayin da Kungiyar Kare Muradin Kabilar Igbo Zalla, Ndigbo ta ragargaji Mamman Daura, saboda furucin kwalelen shugabancin Najeriya da ya yi wa kabilar Inyamurai.
A cikin wata tataunawa da aka yi da Daura, wanda dan uwan Shugaba Muhammdu Buhari ne, ya ce za a yi tsarin shiyya-shiyya ne a zaben shugaban kasa da za a yi a 2023.
A kan haka ne tun kalaman sa ba su gama karade soshiyal midiya ba, Ndigbo ta gaggauta fitar da sanarwar yi wa Mamman Daura tir, ta ke da kiran sa algungumin kitsa bangaranci.
A wata sanarwar da Ndigbo ta fitar a ranar Laraba, kungiyar ta ‘yan kabilar Igbo zalla ta Yankin Kudu, kuma a kudun ma Shiyyar Kudu maso Gabas za a bari su fito da shugaban kasa a zaben 2023, wato kabilar Igbo kenan.
Kakakin Shugaban Kungiyar Kabilar Igbo Zalla, Emeka Attamah ya ce “kalaman Mamman Daura kamar kwalelen shugabancin Najeriya a 2023 ya ke yi wa kabilar Igbo.
“In banda hadama, me ya hana Mamman Daura yin maganar karba-karba tun a 2019.
“Sun game kai sun kori Jonathan, yanzu kuma Daura na yi wa yankin kudu kwalelen wanda zai shugabanci Najeriya a zaben 2023.
“Sai da ya gama tatsar abin da ya tatso daga hannun dan’uwan sa mai shugabancin kasar nan a yanzu, sannan kuma zai fito mana da wani batu ba wanda muka sani ba na karba-karba a 2023.
“Kamata ya yi a matsayin sa na dattijo ya rungumi gaskiya ys rike ta da kyau. Ba wai ya fito jagaliyancin furucin shugabancin kasar nan a 2023 ba, jagaliyancin kuma na nuna son kai da son rai.”