PREMIUM TIMES na dauke da Cikakken raddin martani da Dakataccen Shugaban Rikon EFCC, Ibrahim Magu ya maida wa Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda ya yi zargin cewa shi Magu na satar kudade da kadarorin da ya kwato daga barayin gwamnati.
Magu ya ce shi ba barawo ba ne, kuma bai taba satar ko sisin kwabon kowa ba.
Cikin wasikar da ya aika wa Shugaban Kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa a binciki Magu, ya bayyana cewa Malami na jin haushin sa ne saboda ya yi ta kokarin yi wa aikin EFCC katsalandan, karan-tsaye da kuma uwa-makarbiya a kan wasu kadarori ko kudade da aka kwato. Ya kuma ce Malami ya sha gurgunta kokarin EFCC na dawo da wasu rikakkun masu laifin satar kudade ko zamba, domin a hukunta su.
Dalla-Dallar Raddin Magu Kan Malami:
1. Na ji dadi cikin farin ciki da har Shugaban Kwamiti ka ba ni damar kare ksi na. Dama haka ka’idar adalci a bisa tsarin gudanar da tuhuma ya tanadar.
2. Wannan amsa ko raddi ko kare kai na da zan yi, kamata ya yi a ce na takaita shi.
3.1 A karkashin iko na ban taba ban taba sayarwa ko bari a sayar da wasu kadarorin da aka kwato ba. Ban kuma taba karkatar da kwata kadara ko wasu kudade ba.
3.2 Batun shari’ar harkallar kwangilar P&ID dai alkalan Ingila har yabon EFCC suka yi, kuma da kundin bayanan da EFCC ta rubuta mai shafi fiye da 5,000 ne lauyoyin kasashen waje suka yi amfani wajen kama P&ID da laifi.
3.3 Ko ni ko ita EFCC din kan ta babu wanda ya taba yi wa wani alkali ko jami’in kotu wata barazana yayin gudanar da aikin sa.
3.4 A karkashin jagoranci na ba a ragargaji kukade ko an karkatar da su ko an yi wani abu a kudundune ba.
3.5 Ban taba karkatar da kudade ko kadarorin da aka kwato ba, ballantana har a ce na azurta kai na daga wadannan ksdarori da kudade.
3.6 EFCC na da akidar yin amfani da rubutaccen kwafen bayanai na shaida a dukkan ayyukan da ta ke gudanarwa, ciki har da binciken yadda aka kashe Kudaden Paris Club da duk wasu binciken.
Da Gudumar Gaskiya Ake Ruguza Tubalin Ginin Makaryaci -Magu
4. Ran ka ya dade ka san idan karairayi suka yi yawa, har aka rika maimaitawa ana nanatawa, to babu abin da zai wanke zargi ko wadannan karairayin sai makamin gaskiya kawai.
Wannan shi ne dalilin da zai sa na fito na fede bakin-biri har wutsiya.
Shi Mai Girma Ministan Shari’a da ya rika kitsa min sharri da karairayi, shi ne ma ya rika kokarin dakilewa da gurgunta duk wani kokarin nasarar da EFCC ke yi, ta hanyar yin karfa-karfa ko hana ruwa-gudu a kan wasu bincike ko kadarorin da EFCC ta kwato.
5. Sannan kuma EFCC ta rika samun tsaiko daga Ofishin Ministan Shari’a a kokarin da ya rika yi wajen gurgunta shirin dawo da wasu barayin gwamnati ko mazambata daga kasashen waje domin a hukunta su.
6. Ba kamar yadda aka yi min sharri cewa aikin da na ke yi a EFCC ba na yi da gaske kuma ba na aiki tare da nuna kishin kasa, to ga kwafe-kwafen bayanan tulin nasarorin da na samar a EFCC nan na hado maka da su, domin ka yi alkalanci ka gani.
7. Ran ka ya dade, na fahimci cewa an yi min zargi kan baturuwa shida ne. Don haka ni ma zan rarraba raddi na kan zargin zuwa gida shidan, ina bin su daya-bayan-daya ina amsawa.
Kokawar Malami Da Magu: Wanda ya raba fadan Mai Shari’a Da Dan Sanda bai sha Kallo Ba:
Martanin Ga Rahoton Kwamitin Shugaban Kasa Da Ya Binciki Kudade Da Kadarorin Da EFCC ta Kwato.
1. Ban yarda da sakamakon wannnao rahoto da ya ce an tabka rashin gsskiya, ‘yar-burum-burum da karkatar da kadarori a EFCC ba. Rahoton kirkirarren tuggu ne kawai don a bata min suna kuma a zubar da kimar EFCC.
Karairayi ne kawai aka kitsa mani. Ban saci ko sisin kwabo ba, ban karkatar da ko kadara guda daya ba.
Ina kalubakantar shi wanda ke zargi na ya kawo shaida ko da guda daya ce da ta nuna na karkatar da kudade ko kadarorin da aka kwato a karkashin yaki da cin hanci da rashawa da zambar kudade.
Wannan rahoto algungumanci ne kawai cike fal a ciki. Domin ba a bai wa Hukumar EFCC kwafen zarge-zargen da aka yi mata ba, ballantana a kira jami’an hukumar su kai ko su bayar da bayanin inda ‘yan kwamiti ke tababa, zargi ko Ikirarin an yi ba daidai ba.
Ya zama rahoton rashin adalci, tunda dai ni da ake zargi ba a gayyace ni na kare kai na ba. Wannan kuwa a duk duniya babu inda za a gamsu da irin wannan hukunci, domin ba a ji ta bakin wanda ake zargi ba.
Ni ban taba maida dalolin kudaden da EFCC ta kwato zuwa naira ba a rubuce. Babu inda na kira dala da naira ko sau daya. Idan akwai kuma to a bayar matsayin shaida a kai na.
Ban san inda su ka rakito adadin naira bilyan 39, 357,608, 119 43 ba, suka ce wai na makale kudaden ban saka su cikin adadin kudaden da na ce na kwato ba.
An Kure Ramin Karya:
Shi kan sa magulmacin da ya ce bai hada wa gwamnati da wadannan bilyan 39 da doriya ba, ai ya dawo ya ce kudaden su na Asusun Ajiyar Gwamnatin Tarayya a Babban Bankin CBN.
Wannan kuwa ya karyata duk wani makaryacin da ya ce na karkatar da kudaden ban lissafa da su ba.
Adadin kudaden da Kwamitin Binciken Kudade da Kadarorin Gwamnati da EFCC ta kwato, ya yi azarbabin zargi na da hukumar baki daya da karkatar da kudade. Bai yi la’akari da cewa akwai hukumomi da ma’aikatun da idan an kwato kudaden su da aka sace, to kai-tsaye su ake tura wa kudaden su a cikin asusun su, ba a cikin asusun gwamnatin tarayya na ba-daya da ke CBN ba.
Wadannan hukumomi kuwa sun hada da:
FIRS, NNPC, AMCON, Hukumar Kwastan ta Kasa, Bankunan Kasuwanci, da sauran wasu cibiyoyi da daidaikun jama’a.
Magu ya ci gaba da kan sa tare da hadawa da kwafen takardun hujjoji.
Cikin wadanda ya kara yin magana dalla-dalla, har da yadda jirgin ruwan da EFCC ta kama ya nutse cikin aljihun Malami.
Akwai sauran zarge-zarge da dama wadanda Magu ya rika bi filla-filla ya na cewa karairayi da sharri Minista Abubakar Malami ya yi masa
Cikin su akwai zargin sayar da motoci. Su ma Magu ya karyata tare da kawo hujjoji.
Ya kuma karyata cewa mazambata na ba shi toshiyar baki a shashantar da binciken su.
Sai zargin barun tsohuwar Ministar Harkokin Fetur lokacin Jonathan, wato Diezani Allison-Maduekwe da Magu ya ce ai Malami ne ma ya gurgunta shirin dawo da ita Najeriya domin a hukunta ta.
ABIN LURA: Dukkan zarge-zargen da Magu ke karyatawa, ya na yadawa da kwafen takardun shaidar da ya ce su ke tabbatar da gaskiyar sa.
Haka nan kuma duk wuraren da Magu ya zargi Minista Malami da yi wa EFCC kafar-ungulu, ya na kawo shaidar kwafe-kwafen takardun da ya ke cewa su ne shaidar irin kokarin yankan-,baya da kafar-ungulun da Minista Malami ya rika yi wa EFCC.
Akwai zarge-zargen da PREMIUM TIMES ba ta kawo su a wannan rahoton ba, saboda a baya ta buga rahoton su da kuma raddin da Magu ya mayar a kan su.