2023: Sanata Lawan ya karyata rahoton ya fara shirin takarar shugaban kasa a boye

0

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa rahotonnin da aka yada cewa ya fara kamfen din neman tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023, ba gaskiya ba ne, kuma karya ce gandareriya aka kantara masa.

Ofishin Yada Lawai na Sanata Ahmed Lawan ne ya bayyana wannan raddin a cikin wata takarda da aka fitar daga ofishin a ranar Asabar.

Takardar ta ce, rahoton ya samo tushe ne daga “irin labaran nan ne da ‘yan gida kan bayar, idan sun sha sun yi mankas a mashaya.

“Don haka ya kamata sun wanda ya karanta rahoton, ko ya ji labari daga wanda ya ce shi ma karantawa ya yi, to kawai ya dauki labarin a matsayin surutan bugaggun ‘yan giya a gidan giya kawai.”A ranar Juma’a ce wasu rahotanni (ba a PREMIUM TIMES ba), suka ce Lawan ya fara kici-kicin daura banten kokawar takarar shugabncin kasa a zaben 2023.

Sahara Reporters ce ta buga cewa tuni har Lawal da mukarraban sa sun fara tuntubar manya da kuma kamun-kafar neman maye kujerar shugaban kasa idan. Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin sa a 2023.

“Lawan na ta hakilon neman zama shugaban kasa a 2023 idan har tsarin shiyya-shiyya na karba-karbar shugabancin kasa ya bai wa Yankin Arewa maso Gabas takara.” Inji Sahara Reporters.

Sahara ta kara cewa amma kuma akwai maza a gaban Lawan, domin wasu sun karkata wajen goyon bayan bada takarar APC ga dan Yankin Kudu maso Yamma.

A cikin takardar da Lawan ya ksryata Sahara Reporters, ya ce ai yanzu ba lokacin tunanin fsra wani kamfen ko batun siyasar 2023 ba ne. “Domin a yanzu kasar nan na fama da gagarimar matsala da kalubale masu yawa da ta ke fuskanta.

A karshe ya ja hankalin yin kokari a kauce wa labaran da ke rage wa aikin jarida kima da martaba.

Share.

game da Author