2023: Kungiyar Kabilar Igbo Zalla ta ragargaji Mamman Daura saboda ya yi musu kwalelen shugabancin Najeriya

0

Wata guguwar iskan siyasar shugabancin Najeriya ta kada a ranar Laraba, yayin da Kungiyar Kare Muradin Kabilar Igbo Zalla, Ndigbo ta ragargaji Mamman Daura, saboda furucin kwalelen shugabancin Najeriya da ya yi wa kabilar Inyamurai.

A cikin wata tataunawa da aka yi da Daura, wanda dan uwan Shugaba Muhammdu Buhari ne, ya ce za a yi tsarin shiyya-shiyya ne a zaben shugaban kasa da za a yi a 2023.

A kan haka ne tun kalaman sa ba su gama karade soshiyal midiya ba, Ndigbo ta gaggauta fitar da sanarwar yi wa Mamman Daura tir, ta ke da kiran sa algungumin kitsa bangaranci.

A wata sanarwar da Ndigbo ta fitar a ranar Laraba, kungiyar ta ‘yan kabilar Igbo zalla ta Yankin Kudu, kuma a kudun ma Shiyyar Kudu maso Gabas za a bari su fito da shugaban kasa a zaben 2023, wato kabilar Igbo kenan.

Kakakin Shugaban Kungiyar Kabilar Igbo Zalla, Emeka Attamah ya ce “kalaman Mamman Daura kamar kwalelen shugabancin Najeriya a 2023 ya ke yi wa kabilar Igbo.

“In banda hadama, me ya hana Mamman Daura yin maganar karba-karba tun a 2019.

“Sun game kai sun kori Jonathan, yanzu kuma Daura na yi wa yankin kudu kwalelen wanda zai shugabanci Najeriya a zaben 2023.

“Sai da ya gama tatsar abin da ya tatso daga hannun dan’uwan sa mai shugabancin kasar nan a yanzu, sannan kuma zai fito mana da wani batu ba wanda muka sani ba na karba-karba a 2023.

“Kamata ya yi a matsayin sa na dattijo ya rungumi gaskiya ys rike ta da kyau. Ba wai ya fito jagaliyancin furucin shugabancin kasar nan a 2023 ba, jagaliyancin kuma na nuna son kai da son rai.”

Share.

game da Author