Za a sallami duka ‘yan N-Power, za a dibi sabbi daga watan Yuni – Gwamnati

0

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana shirin sallamar duka wadanda ke shirin tallafi na N-Power a kasar nan.

Gwamnati ta ce za ta dibi sabbi idan ta sallami wadanda suke cikin shirin yanzu.

Kakakin ma’aikatar jinkai, Rhoda Iliya ta ce wadanda suke rukunin A za su yi sallama da shirin a 30 gawatan Yuni, sai kuma rukunin B za su yi sallama da shirin a karshen watan Yuni.

Bayan wadannan rukuni sun yi sallama da shirin za a dauki sabbin matasa a sabon rukuni na C da za su fara aiki daga 26 ga Yuli.

” Gwamnati za ata sanar da sabbin matakai da za a bi wajen shiga shirin da za a fara na sabbin rukunonin A da B nan ba da dadewa ba. Sannan kuma duk wanda ya amfana da shirin a baya ba za a dauke shi a sabbin rukunonin shirin na A da B ba.

” Za a bude shafin cika fam daga ranar 26 ga watan Yuni domin daukar sabbin wadanda za su mori shirin.

” Zuwa yanzu muna tsara yadda za a dauki wasu daga cikin wadanda suka mori shirin a baya ta hanyar koya musu sana’o’i da basu jari, sannna kuma yi wa kamfanoni masu zaman kansu tayin su domin su dauke su aiki.

Share.

game da Author