Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna takaicin sa karara dangane da mummunar asarar rayukan da aka yi a Katsina da Barno cikin makon nan, inda ‘yan bindiga da Boko Haram suka kashe kusan mutum 200 cikin kwanaki uku.
A jawabin da ya karanta a Ranar Zagayowar Dimokradiyya da kuma cikar mulkin dimokradiyya shekaru 21 a jere ba tare da katsalandan din sojoji ba, Buhari ya nuna alhini, jimami da ta’aziyyar sa ga wadanda abin ya shafa da kuma kasa baki daya.
A jawabin na sa, Buhari ya nuna cewa dukkan hare-haren biyu, an yi amfani da halin zaman gidan da jama’a ke ciki ne aka kai wa jama’a harin.
Ya ce ya bada umarni ga jami’an tsaro a gaggauta kamo wadanda suka yi wannan aika-aika domin a hukunta su.
Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihohi da kananan hukumomi su kara karfafa tsarin leken asirin fallasa batagari da mugaye a cikin jama’a a duk inda aka gan su ko aka ji duriyar su.
Da ya koma kan Boko Haram, Buhari ya ce gwamnatin sa ta yi nasarar kwato dukkan wasu yankuna a kananan hukumomin da Boko Haram suka mamaye.
Ya ce a yanzu babu wata karamar hukuma da ke hannun Boko Haram, kuma wadanda suka gudu daga garuruwan su na ta komawa gida, saboda tsaron da ya kara Inganta.
Buhari ya ce tsaro ya kara inganta a Yankin Neja Delta, ta yadda aka dakile manyan ‘yan bindigar da ke bumburutun danyen man fetur.
Premium Times ta buga labaran yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da yi wa mazauna yankunan karkara kisan-,kare-dangi a jihar Katsina da Sokoto da Zamfara.
Haka kuma wannan jarida ta buga labarin yadda Boko Haram suka yi wa mutum 81 kisan kiyashi a yankin Karamar Hukumar Gubio, cikin jihar Barno.