Gwamnatin jihar Barno da hadin guiwar kungiya mai zaman kanta ‘North East Regional Initiative (NERI)’ Za su gina gidajen radiyo hudu a jihar.
Kwamishinan yada labarai, al’adun gargajiya da harkokin cikin gida, Babakura Abba-Jato ya sanar da haka ranar Litini a bikin cika shekara daya da gwamna Babagan Zulum yayi a jihar Barno.
Abba-Jato ya ce a yanzu haka an bude gidan radiyo a garin Biu dake aiki a kullum a garin.
Ya ce za a bude sabbin gidajen radiyon a garuruwan Monguno, Damasak da garin Dikwa.
Abba-Jato ya ce gwamnati ta samar da na’uran yadda labarai domin inganta aiyukkan gidan rediyon da talabijin din Barno (BRTV).
” Za kuma mu saka tashar gida talabijin din mu a tauraron dan adam domin mutanen dake kasashen waje su kallon mu kai tsaye, al’adu da shirye-shiryen da aka yi a jihar.
“Gwamnati za ta kuma farfado da gidan buga jaridar jihar da ya dade baya aiki.