‘Yan sanda sun samu rahotannin fyade 717 cikin watanni biyar -Sufeto Janar Adamu

0

Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayyana cewa an samu rahotannin fyade har sau 717 tsakanin watan Janairu zuwa karshen Mayu, 2020.

Da ya ke wa manema labarai karin bayani a Fadar Shugaban Kasa, Adamu ya shaida musu cewa ya gana da Buhari ne kuma ya yi masa karin haske dangane da ratotannin cin zarafin mata a kasar nan.

Ya ce a cikin wadannan watanni biyar an damke mutum 799 da aka zarga da laifin cin zarafin mace.

Adamu ya ce daga cikin 799 din nan, ‘yan sanda sun kammala binciken 631 kuma tuni an gurfanar da su a kotu.

“Sauran mutum 52 kuma ana nan ana ci gaba da binciken su

“Dokar zaman-gida-tilas da hana zirga-zirga ce ta kara haddasa wannan. Amma dai tun kafin annobar Coronavirus ana samun rahotannin fyade a kasar nan.”

Ya roki jama’a su rika kai wa ‘yan sanda rahotannin fyade da duk wasu nau’uka na cin zarafin kananan yara da Mata.

Share.

game da Author