‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta sun damke wani fasto da ake zargin yayi lalata da ‘yar shekara 19 da karfin tsiya.

Komandan rundunar Mohammed Garba ya sanar da haka wa manema labarai ranar Litini a garin Warri.

Garba ya ce rundunar ta kama shugaban cocin ‘Victory Revival Fasting and Prayer Ministry’ dake Warri bishop Elijah Orhonigbe da ake zargi da yin lalata da ‘yar shekara 19 da karfin tsiya.

Ya ce sun kama shugaban cocin ne bayan mahaifiyar yarinyar ta kawo kara ofishin ‘yan sanda.

Garba ya ce mahaifiyar yarinyar ta shaida wa ;yan sanda cewa wannan fasto ya gargadesu cewa yayi mafarki ya ga mutuwa na kai komo a gidan su. daga nana sai ya umarci matan ta gaggauta kawo yarta a yi mata addu’a na musamman saboda a kori wannan mutuwa dake shawagi a gidan su.

Cikin gaggawa wannan mata ta kawo masa ‘yar tata domin ayi mata addu’a. bayan Addu’ar sai faston ya gudu. Sai da yarinyar tayi kwana biyu bata cikin hayyacin ta koda muka kaita asibiti.

‘Yarinyar ta fadi da kanta cewa faston ya bata man Zaitun ta shafa a gabanta sannan ya bata wani jiko ta kwankwada daga nan sai ya ce ta kwanta a wani tabarma zai fara aikin addu’a. Tun daga lokacin ta fita daga hayyacin ta bata san inda take ba.

Duk da cewa ‘yan sanda sun samu bayanan gwajin da likitoci suka yi wa wannan yarinya da suka nuna lallai an sadu da ita, fasto dai yace sam-sam bai aikata wannan laifi ba.

Ya shaida wa kotu cewa tabbas yayi wa wannan yarinya addu’a amma fa a gaban wasu mutum uku yayi mata. tun bayan nan ba sake ganin ta ballantana wai har ya yi lalata da ita.

Ya ce sam bai yarda da wannan zargi ba kuma shima a shirye yake a je ko-ina za a je indai akan maganar yayi wa wannan yarinya fyade ne.

Haka ita uwar ‘ya ta ce a shirye take sai an kwato wa ‘yarta hakkin ta.

Share.

game da Author