‘Yan Najeriya sama da milyan 100 ba su da katin shaidar dan kasa -Shugaban Rabon Kati

0

Shugaban Hukumar Raba Katin Shaidar Dan Kasa (NIMC), Aliyu Aziz, ya bayyana cewa akalla sama da mutum milyan 100 har yau ba su mallaki katin dan kasa da a Turance ake kira ‘National ID Card’ ba.

Aziz ya bayyana haka ne a wata ganawa da editoci da ya yi a Abuja, ranar Laraba.

Ya lissafa rukunin mutane kusan goma da ya ce su ne har yanzu ba su samu sukunin mallakar wata shaidar katin dan kasa ba.

Wadanda ya lissafa sun hada da talakawa fitik, mata da kananan yara wadanda ba su da galihu, masu karancin ilmi, masu gudun hijira, masu yin kaura daga wuri zuwa wani wuri, masu neman mafaka, musakai da fakirai da kuma dimbin mazauna kauyuka da yankunan karkara.

“Akalla akwai mutum milyan 200 a Najeriya, Amma kashi 38% kadai suka mallkaki wata shaida mai nuna cewa su ‘yan Najeriya ne..

“Zuwa yanzu an damka wa mutum milyan 41.5 lambar shaidar rajistar katin dan kasa, wato NIN tun daga 2012 zuwa yau.”

Aziz ya kara da cewa cikin wadanda aka raba wa lambar har da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare da kuma wadanda suka mallaki takardar iznin zama Najeriya.

A karshe ya ce NIMC ta yi hadin guiwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), NTA, NOA da wasu kafafen yada labarai domin wayar da kan jama’a sanin muhimmancin mallakar katin dan kasa.

Share.

game da Author