Kwamishinan ‘yan sannan jihar Neja Adamu Usman ya yi kira ga mutanen jihar da su hada hannu da Jami’an tsoro domin ganin an damke maharan dake garkuwa da mutane, satan shanu da kisan mutane a jihar.
Usman ya yi wannan kira a ranar Alhamis yayin da rundunar ke tura jami’ai da zaratan ‘yan banga domin samar da tsaro a garin Mariga, Kanfanin Bobi da Kasuwar Garba dake karamar hukumar Mariga.
Ya ce rundunar Za ta bukaci bayanai daga wajen mutane da zai taimaka wajen kama masu aikkata miyagun aiyukka a jihar.
Usman ya ce dakile hare-haren mahara zai taimaka wajen samar da tsaro kuma manoma zasu koma gona gadan-gadan ba tare da fargaba ba.
“Jami’an tsaro ba za su yi kasa-kasa ba wajen ganin sun bankado masu aikata miyagun aiyuka irin haka a jihar.
“Muna kira ga masu ruwa da tsaki da su mara mana baya a aiyukkan samar da tsaron da Za mu yi sannan za kuma mu karfafa gwiwowin mutane domin su iya fitowa da bayanan da Za su taimaka wajen kawo karshen muyagun aiyyuka a jihar.
Kwamishinan kananan hukumomi da sarakunan na jihar Abdul Malik Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ta gama shiri tsaf domin ganin Jami’an tsaro sun gudanar da aiyukkan su yadda ya kamata.
“Mun kebe sansanoni da ‘yan San da da ‘yan banga za su yi amfani da su yayin da suke gudanar da aiyukan su.
A karshe ya ce gwamnati na ganawa da sarakuna domin su bada nasu gudunmawar su wajen kau da matsalar rashin tsaro a yankunan su.
Discussion about this post