YAKIN BIAFRA: Dalilin da ya sa kabilar Igbo ba su daina korafi, kulafuci da kurari ba – Jagoran Ohanaeze

0

Jagoran Kungiyar Kare Muradun Kabilar Igbo Zalla, wato Ohanaeze, Nnia Nwodo, ya ce shekaru 50 bayan kammala Yakin Basasa wanda ya ci rayukan milyoyin jama’a, har yau kabilar su ta Igbo ba ta daina korafi, kulafuci da karaji ba, saboda gwamnatocin da suka gabata ba su warware matsala da dalilan da suka haddasa barkewar yakin ba.

Nwodo ya na magana ne a matsayin sa ba bako sa Sashen Igbo na BBC ta gayyata a ranar Asabar domin tattauna batun Yakin Biafra.

A ranar Asabar din ce aka cika shekaru 50 da kammala Yakin Basasa, wato Yakin Biafra.

Nwodo ya ce har yau gwamnati ba ta warware matsalolin da suka haddasa yakin ba. Dalili kenan su kuma kabilar Igbo ake kallon cewa ba za su taba daina kurari, karaji, korafi da kulafuci ba.

Ya tunatar da irin hazikancin kabilar Igbo, inda ya ce a lokacin Yakin Biafra har filin jirgi suka gina, kuma suka kera jirgin yaki.

A ranar 30 Ga Mayu, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin ydda Coronavirus ta hana IPOB bukukuwan tuna cikar Yankin Biafra shekaru 50

Kabilar Igbo musamman ‘yan Kungiyar Taratsin Kafa Biafra (IPOB), sun sha alwashin yin bukukuwan tunawa ko tayar da tsohon mikin da yankin Basasa ya yi musu, wanda a yau Asabar, 30 Ga Mayu ne aka cika shekara 50 daidai da kawo karshen yakin.

Sai dai kuma masu goyon bayan Biafra din a wannan shekarar ba su samu yadda su ke so ba, saboda barkewar Coronavirus a duniya ta rage wa ranar tunawar ta su karsashi da armashi.

Dama dai a baya, kowace shekara ‘yan IPOB kan gudanar da zanga-zangar da sau da dama ba a wanyewa lafiya.

An sha yin arangama da jami’an tsaro har ana kashe da dama daga cikin su.

A shekarar 2018 jihohin Kudu maso Kudu sun rufe kasuwanni rif a ranar 30 Ga Mayu. Amma a 2019, umarnin a rufe din bai shiga kunnen yawancin ‘yan kasuwar jihohin ba.

A wannan shekarar ta 2020 kuwa, maimakon zanga-zanga ko umarnin zaman-gida, Kungiyar IPOB ta roki kowa ya yi azumin kwanaki uku tare da yin addu’o’i.

Haka Sakataren IPOB, Emma Power ya sanar cewa “kowa ya gudanar da azumin kwanaki uku, kuma ya yi addu’o’i.”

Yakin Biafra A Takaice: Dalilai Uku Na Barkewar Yaki

1. Juyin mulkin 15 Ga Janairu, 1966 wanda ‘yan Arewa suka fassara da cewa kabilar Igbo ne suka kashe manyan shugabanni da sojojin Arewa.

2. Juyin mulkin Mayu, 1966, wanda kabilar Igbo suka fassara da cewa ramuwar-gayya ce sojojin Arewa suka yi.

3. Kisan-rubdugun da aka rika yi wa kabilar Igbo bayan juyin mulkin 1966.

Tarihin Yakin Basasar Watanni 30:

1. Janairu, 1966: An kashe su Sardauna da su Tafawa Balewa.

2. Janairu, 1966: An nada Ojukwu Gwamnan Yankin Gabashin Najeriya.

3. Yuli, 1966: Su Murtala sun yi wa Ironsi juyin mulki, suka nada Yakubu Gowon sabon Shugaba.

4. Yuni Zuwa Oktoba, 1966: Hargitsi a Arewa, wanda ya haifar da kisan kabilar Igbo.

5. Mayu, 1967, Ojukwu ya yi ikirarin kafa ‘Jamhuriyar Biafra, tare da shelar ballewa daga Najeriya.

6. Yuli, 1967: Yakin Basasa ya barke.

7. Oktoba, 1967: Sojojin Najeriya sun ci Enugu, hedikwatar Biafra da yaki.

8. Mayu, 1968: Sojojin Najeriya sun ci Fatakwal da yaki.

9. Afrilu, 1969: Sojojin Najeriya sun kwace garin Umuahia.

10. Janairu, 1970: Ojukwu dan tawaye ya tsere gudun hijira.

11. Janairu, 1970: Biafra ta yi saranda.

Share.

game da Author