Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya yi kira ga Kungiyar likitoci (NARD) da su tausaya su janye yajin aiki da suka fara cewa rashin yin haka zai sa a rasa rayukan mutane da dama a kasar nan.
Likitoci dake karkashin Kungiyar NARD likitoci ne dake koyan aiki likitanci a asibitocin kasar nan.
Wadannan likitoci su ne suka fi yawa a likitocin da ake da su a kasar nan sannan suna cikin ma’aikatan dake kula da masu fama da cutar coronavirus a kasar nan.
Idan ba a manta ba a ranar Litini ne Kungiyar NARD ta Sanar cewa ta fara yajin aiki gama a kasar nan.
Kungiyar ta ce rashin biyan su albashi da alawus din su da rashin kayan kare ma’aikatan kiwon lafiya daga kamuwa da cutar Covid-19 na daga cikin dalilan da ya sa suka fara yajin aiki.
Ma’aikatan lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta samar musu kayan aiki musamman wanda ke kare ma’aikatan daga kamuwa da cuta amma kadan daga cikin ma’aikatar ne aka iya samar wa kayan aikin.
Sai dai shugaban Hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce gwamnati ta samar wa ma’aikatan kiwon lafiya isassun kayan aiki a kasar nan.
Fargaban Ministan kiwon lafiya
Minista Ehanire ya ce yajin aiki da likitocin suka fara na iya kawo wa fannin kiwon lafiya kasar nan matsalar gaske.
A zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 ta yi tare da wakilan Kungiyar NARD Ministan lafiya ya yi kira ga Kungiyar da ta yi hakuri ta janye yajin aiki aiki da suka fara.
“Ina tabbatar muku da cewa gwamnati za ta biya duk bukatun kungiyar wanda a ciki akwai samar musu da horo na musamman da samar da kayan aiki kare duk wani ma’aikacin asibiti a kasar nan.