Ma’aikatar tsaron Najeriya ta bayyana yadda zaratan dakarun Najeriya suka darkake kuma suka dakile harin Boko Haram bangaren ISWAP a gumurzun da suka yi da su a Monguno.
Dakarun Najeriya sun kashe Boko Haram 20 a wannan arangama.
Kodinatan yada labarai na ma’aikatan tsaron Najeriya, John Enenche ya shaida cewa zaratan kasa da sama suka dirawwa Boko Haram din kuma bayan kashe mutum 2O da suka yi, sun kwato motocin yake hudu sannan sun cafke da yawa daga cikin su.
Haka shima babban hafsan sojojin Najeriya Tukur Buratai, ya jinjina wa sojojin da suka fafata da Boko Haram din sannan ya yi alkawarin ci gaba da fatattakar sojojin har sai sun gama da su.
Bayan haka ya ce mahara da ‘yan bindigan da suka addabi jihohin Katsina, Zamfara da sauran sassan Arewa maso Yamma, suma su su kwana da shirin da sauraren luguden sojojin Najeriya wadda shi kansa a shirye yake ya diran musu.
Idan ba a manta ba, a jawabin shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ranar Dimokradiyya, shugaba Buhari ya jaddada wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin sa za ta gama da Boko Haram nan ba da dadewa ba sai dai kuma, jim kadan bayan furta haka Boko Haram suka sake afkawa kauyen Gubio, sun kashe mutum 31.
Buhari ya yi wannan kuri ne bayan maharan sun afkawa kauyen Gubio inda suka kashe mutum sama da 80 a hari daya. Bayan haka sun dira Mungono bayan haka, nan ma an dauko rahotan yadda suka kashe mutum 13.
Sai kuma sabon hari da suka kai garin Gubio a karo na biyu duk a tsakanin mako daya inda suka kashe mutum 31.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan sun rika raba takardar gargadi ga mazauna garuruwan dake yankin Gubio da su daina kare sojojin da da biye musu.
” Takardar da da suka rubuta da harshen Hausa, ta ce Boko Haram bangaren ISWAP ba ruwanta mutane idan basu tare da sojoji. Cewa Sojoji suke hari ba mutane amma wanda ya biye wa sojoji shima zai dandana kudar sa.
Mazaunin ya ce maharan sun bi kauyukan dake zagaye da Gubio da Monguno suna raba musu wannan takardar sako.