Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar kira ga gwamnati ta inganta tsaro a kasar nan da aka yi a jihar Katsina Bishir Dauda ya bayyana yadda jami’an ‘yan sanda suka tsare Nastura Sharif sannan suka auna dashi har Abuja.
Dauda ya bayyana cewa bayan sun gama zanga-zangar sai suka dunguma zuwa hedikwatar ‘Yan sanda domin yi musu godiyar kariyar da jami’an su suka ba masu zanga-zanga tun daga farko har karshe.
” Muna tsaye muna tattaunawa da Kwamishinan ‘yan sandan jihar da mika godiyar mu kuma ya amshe mu hannu bibbiyu, sai kuma ya shaida mana cewa Nastura zai bishi zuwa Abuja, cewa sufeto janar Mohammed Adamu na son ganin sa.
” Nastura ya nemi ya tafi a motar sa amma Kwamishina ya ce, Sufeto Adamu ya ce su taho a motar ‘yan sanda.
Dauda ya kara da cewa isar su Abuja ke da wuya sai aka tsare shi.
An saki Nastura da yammacin Alhamis.
Idan ba a manta Nastura da wasu sun gudanar da zanga-zangar lumana a darin Katsina domin yin kira ga gwamnati da jami’an tsaron Najeriya su kawo wa mutanen jihar dauki game da hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi sassan jihar da dama.
Jihar Katsina da Jihohin dake makwabtaka da ita kamar su Kaduna, Zamfara da Neja na fama da hare-haren yan bindiga da masu garkuwa.
‘Yan bindiga kan far wa gari su bude wuta. Su kashe na kashe, su yi garkuwa da wasu.
Discussion about this post