Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa ta gano gawar wani saurayi da budurwarsa a wani gida dake Ilasan, a jihar.
Binciken da suka yi bayan gano wannan gawarwaki ya nuna cewa gawar namijin dai sunan sa Olamide Alli mai shekaru 25, da Chris Ndukwe, mai shekaru 39 a wannan gida da aka gano gidan marigayi Olamide Alli ne.
Kakakin rundunar Bala Elkana ya Sanar da haka yana mai cewa sun iske Chris kwance male-male cikin jini shi kuma Ali kumfar mutuwa a bakin sa.
“Akwai yiwuwar cewa Alli ne ya kashe budurwarsa Chris da wuka sannan shi kuma kwalkwali ruwan guba ya kashe kansa.
“Mun ga wukake guda biyu da jini a jikin su, roban maganin sniper guda biyu da gwangwanin lemon red bull guda biyu a dakin.
Elkana ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano yadda wadannan mutane suka mutu.
Bayan haka wasu da suka san Chris da Alli sun bayyana wa rundunar ‘yan sandan cewa Alli da Chris saurayi da budurwa ne kuma suna da ‘ya’ya Maza biyu tare amma babu aure tsakanin su.
Wata kanwar Chris da suka zo gidan Alli tare ta ce Chris da Alli sun dade tare sannan sun saba fada su na shiryawa.
Kawar ta ce karar sauti daga dakin da Chris da Alli suka kwana ya tashe ta, daga nan sai ta mazamaza ta keka dakin ta ga me ke faruwa, tana shiga kuwa sai ta same su su biyu suna shure-shuren mutuwa.