Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

0

Babban Hafsan Sojojin Sama Mashal Abubakar Sadiq, ya bayyana cewa sojojin Operation Wutar Daji sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga 10 a jihohi hudu na Arewa maso Yamma.

Sadiq ya yi wannan bayani ne a ranar Talata a Katsina, lokacin da ya kai ziyara domin duba ayyukan rundunar, wadda ya ce ba ta fi wata daya da kafawa ba.

Ya ce jiragen yaki 10 aka ware domin kai wannan farmakin murkushe ‘yan bindiga a jihohin Kebbi, Katsina, Zamfara da Kaduna.

“An yi amfani da jiragen yaki 10 wajen tarwatsa sansanin ‘yan bindiga a Kuyambana, Dajin Rugu, Birnin Gwari da Dansadau.

“Dakarun mu na leken asari sun hango mabuyar ‘yan bindiga da dama. An gagargaje sansanonin, an kashe da dama daga cikin su.”

“Ina sanar da cewa wannan fatattakar mahara da ake kan yi, ba za a sassauta ba har sai an kakkabe dukkan masu hai hare-haren baki daya.

“Za mu ci gaba da fatattakar mahara har sai ta kai baby sauran wani dan bindiga a jihohin Arewa maso Yamma da sauran sassan kasar nan baki daya.

Daga nan ya ziyarci wurin ajiyar jiragen yaki da ake ginawa domin kare jiragen daga kwaleliyar ranar da suke sha, a inda suke ajiye.

Sadiq ya ce barin su da ake yi a rana na kawo nakasu wajen yi musu garambawul.

Share.

game da Author