Gidauniyar ‘CLEEN Foundation’ ta fadi yadda sojoji suka kashe wata gyatuma mai tuwo-tuwo da dukan tsiya wai don ta ki zama cikin gida bayan saka dokar Kulle da gwamnatin jihar Nasarawa ta saka.
Da ya ke yi wa PREMIUM TIMES karin bayani shugaban gidauniyar Anna White-Agbo ta shaida cewa sojojin sun fito korar wadanda suka fito a lokacin da aka saka dokar Zaman Gida Dole ne.
” Sojojin sun yi ta korar mutane su koma gida da bulala, da suka tinkari wannan mata ita kuma ta ce ba za ta tafi gida ba sai ta saida abincin domin basu da komai a gida. Daga nan sai suka hau ta da duka har sai da ta mutu.
An ce an sanarwa rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa. Sai dai kuma kakakin rundunar Ramhan Nansel, ya ce bashi da masaniya game da haka.
Ita dai wannan gyatuma mai saida abinci na daga cikin mutum 36 da CLEEN tace an kashe su a fadin Najeriya tun da aka saka dokar Zaman Gida Dole a jihohin kasar nan da kuma dokar hana tafiye-tafiye.
Kakakin rundunar Sojoji, Sagir Musa bai amsa kira da sakonni da aka aika masa ba game da wannan zargi.
” A jihar Legas, a ranar 20 ga Mayu ‘yan sanda sun kashe wani Fatai Oladipupo cikin kuskure a kokarin tabbatar da mutane sun bi dokar kulle a titin Igando, Ikotun, Legas.
” A jihar Anambra jami’an tsaro sun kashe wani matashi da ya karya dokar zaman gida dole. Hakan ya faru ne a Enugwu-Ukwu dake karamar hukumar Njikoka.
” Haka kuma wakilin CLEEN ya sahida cewa an kashe mutane a sanadiyyar jaddada dokar Zaman Gida Dole da gwamnati ta Saka.
Haka kuma a jihar Ribas, gwamnan jihar Nyesom Wike ya kama wasu matafiya 14 da suka dauko shanu daga tireloli biyu zuwa jihar. Bayan kama su da yayi ya saka a yi wa mutane gwanjon shanun nan take.
A jihohin Nasarawa, wasu sassan Abuja, Benuwai da wasu jihohin kasar nan suna gudanar da al’amurorin su yadda suke so, bukukuwa, taro, da sauran su.