Yadda Oshiomhole ke kokarin daure gindin mutumin da ya ce ba abin bai wa amanar kudi ba ne, zama gwamnan Edo

0

Bisa dukkan alamu dai a yanzu Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, kuma tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya sha giyar siyasa mai ribas, inda ya fito yanzu ya ke goyon bayan mutumin da ya kira “wanda bai cancanci a damka wa amanar kudi ba”, domin ya zama gwamnan jihar a zabe mai zuwa.

Oshiomhole a yanzu ya na goyon bayan Osagie Ize-Iyamu, wanda a zaben 2016 ya tsaya takarar gwamna a karkashin PDP.

A wancan lokacin Oshiomhole ya kammala wa’adin shekara takwas, amma ya na goyon bayan Obaseki na APC ya zama gwamna.

Shi ma Ize-Iyamu tsohon dan APC ne, domin ya yi wa Oshiomhole Daraktan Kamfen a lokacin ya na takarar gwamna a baya.

Sabanin siyasa ya sa ya koma PDP ya tsaya takara a karkashin ta, a zaben 2016.

A lokacin wancan zabe na 2016, Oshiomhole ya matsayin sa na gwamna mai barin gado, ya rika yi wa Ize-Iyamu yarfe cewa ba mutumin kirkin da za a bai wa amanar kudi ba ne.

Bayan Obaseki ya zama gwamna, ya samu mummunan sabani tsakanin sa da tsohon ubangidan sa, Oshiomhole.

Dalili kenan a yanzu shi Oshiomhole ya rakito Ize-Iyamu, ya dawo APC, sannan kuma ya ke neman tsaida shi takarar zaben gwamna a APC, maimakon mara wa Gwamna Obaseki.

Jam’iyyar APC ta afka cikin rudani a jihar Edo, ta kai ga yanzu haka har yau ba a kaddamar da ‘Yan Majalisar Dokokin Jiha su 14 ba, tun bayan rantsar da su a cikin Tuni, 2019.

Lokacin kamfen din 2016, Oshiomhole ya rika kiran dan takarar PDP Ize-Iyamu, “mutumin banza”, wanda ba abin a bai wa amanar kudade ba ne.”

“E tabbas da a tare muke kafin mu ya koma PDP. To amma lokacin da ya yi min dakatan kamfen, bayan na ci zabe ai ban ba shi kowane irin mukami ba.

“Ai na san halin kaya na, shi ya sa ban yarda na amince na ba shi mukamin siyasa ba. Sai na bar shi ya na yi min jagaliyanci da kulle-kullen tuggun siyasa a tsakar dare.

“Domin na san shi sarai, ba mutumin da ya kamata a damka wa amanar kudi ba ne.

“Saboda haka akwai hatsari idan al’ummar jihar Edo su ka zabi wannan mutumin (2016) ya zama gwamna.

“Ni ina kira a zabi Obaseki, mutumin kirki, nagari kuma mai amana da fikirar kirkiro hanyoyin ci gaba.” Inji Oshiomhole.

PREMIUM TIMES ta mallaki bidiyon da Oshiomhole ya rika muzanta Ize-Iyamu, amma kuma a yanzu shi ne ya ke so ya zama gwamna a Edo, a zaben da za a yi cikin Satumba mai zuwa.

An tambayi kakakin Ize-Iyamu, mai suna John Mayaki dangane da aibata Iyamu din da Oshiomhole ya taba yi, sai ya ce, wannan ai ba wani abu ba ne son sun dawo sun sake hadewa a yanzu.

Ya rika buga musali yadda Bola Tinubu ya rika sukar Shugaba Muhammadu Buhari a baya, amma a yanzu su na inuwar siyasa daya.

Ya kawo misalin yadda Obasanjo ya goyi bayan Goodluck Jonathan, amma daga baya ya kware masa baya.

Ya buga misalin yadda Obasanjo ya kware wa Atiku Abubakar Baya, amma a zaben 2019 ya mara masa baya.

Share.

game da Author