Yadda matashi ya kashe matar wan sa bayan yayi lalata da ita da karfin tsiya a Gusau

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta damke wani matashi mai suna Aminu Bala dake da shekaru 25 a duniya da laifin kashe matar wansa bayan yayi lalata da ita da karfin tsiya a garin Gusau.

Kakakin rundunar, Mohammed Shehu ya shaida cewa Aminu ya amsa laifin sa bayan kama shi da ‘yan sanda suka yi.

Aminu dan asalin kauyen Damaga dake karamar hukumar Maradun amma kuma mazaunin rukunin gidaje na Damba kwatas a garin Gusau.

‘Yan sanda sun ce da misalin karfe 4 na yammacin litinin aka kira su cewa wani ya kashe matar wansa a kwatas din Damba.

Isar su ke da wuya sai suka iske matar wan, wannan matashi kwance malemale cikin jini da sarar adda a jikin ta.

Ko da aka kaita asibitin Yariman bakura dake Gusau likitoci sun ce ta riga ta cika.

Shehu ya kara da cewa ba samu damar gudanar da komai ba bayan tsare wannan matashi da aka yi saboda mijin wannan marigayiya baya gari, yayi tafi. Amma kuma ya shaida wa ‘yan sanda ta wayar tarho cewa kanin shi Aminu ya dade yan yi wa matar sa barazanar sai ya kashe ta.

Share.

game da Author