Dan majalisan dake wakiltar Karamar hukumar Sabuwa a majalisar jihar Katsina a majalisar tarayya ya bayyana yadda mahara suka far wa kauyen Sabuwa suka kashe mutum tara sannan suka sace shanu 500.
Danjuma ya ce ranar Asabar wadannan mahara dauke da manyan bindigogi kan babura suka kai hari Sabuwa daga kauyen Tashan Bawa kafin suka koma mabuyar su a daji.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba na wannan mako ne PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda mahara suka kashe mutum 20, wasu mutum 20 suka ji rauni a jikinsu a harin da suka kai a karamar hukumar Faskari.
Danjuma ya ce a cikin wata daya mazaunan karamar hukumar Sabuwa sun tsere daga matsugunin su a dalilin hare-haren maharan.
“A ranar Asabar maharan sun kashe mutane a kauyen Tashan Bawa, daga nan sai suka zarce kauyen Yarkaka suka kashe mutum biyu, suka ji wa mutum 4 rauni sannan suka isa kauyen Unguwan Dauda, nan ma suka kashe mutum daya suka kone motoci biyu.
Ya ce mahara sun kuma fatattaki mazaunan kauyen Tashan Labbo, sun kone babur daya, sun kuma kashe mutane da dama sannan suka sace kaya a shagunan mutane a kauyen Gamji.
Danjuma ya ce mahara sun saci babura a kauyen Kanawa, sun kashe mutum uku a kauyen Taura sannan a kauyukan Nakaba da Idaki maharan sun sace shannu da dama suka kashe mutum uku kafin suka koma maboyar su a daji da misalin karfe 3 na dare.
” Na sanar wa Jami’an tsaro a lokacin da maharan ke aikin azabtar da mutane amma babu jami’in tsaron da ya kawo musu dauki.
Danjuma ya ce za a yi fama da yunwa a jihar Katsina da kasa baki daya idan gwamnati basu yi maza-maza sun kawo wa manoma da mutanen gari dauki ba.