Kungiyar Kirkiro Hanyoyin Samar da Abinci da Matakan Kare Gurbacewar Muhalli (GEFSEP), ta bijiro da hikimomin zaburar da jami’a a duniya su dukufa wajen noma kayan miya, kayan marmari da nau’ukan abinci a lambu na cikin gida ko bayan gida domin samun wadatar abinci.
Kungiyar ta kasa-da-kasa, GEFSEP, ta ce yin lambu a gida babbar hanya ce ta samar da kayan abinci, kayan miya da kuma kayan marmari, yadda yadda za a kauce wa matsalar karancin abinci.
GEFSEP kungiya ce mai zaburarwa, ilmantarewa da kuma bunkasa kare muhamli ta yadda al’umma za ta samu ci gaba.
An kafa kungiyar ce domin tunkarar gagarimin kalubalen gurbacewar muhalli, sauyi ko canjin yanayi, sai kuma bunkasa kananan harkokin noma domin samar da abinci da kare muhalli.
“Ganin yadda matsalar karancin abinci ya tunkari duniya gadan-gadan, sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus, ya zama dole mu tashi tsaye, ba kawai mu yi aiki da kwakwalwa ko tunanin mu ba, har ma da aiki da hannayen mu domin mu yi dukkan kokarin hana yunwa ko karancin abinci su yi mana shigar-bazata.”
Haka Babban Daraktan kungiyar GEFSEP, David Terungwa ya bayyana a karshen makon nan.
Dalilin haka ne GEFSEP ta kirkiro shirin yin lambuna a gidaje domin noma kayan marmari na itatuwa, kayan abinci da kuma kayan miya.”
Ya kara Jan hankalin masu gidaje su yi lambunan domin su amfana, Terungwa ya ce akwai matukar bukatar jama’a su rika samar wa kan su kayan marmari da abinci mai gina jiki, musamman kayan miya a wannan lokacin da cutar Coronavirus ke ci gaba da yi wa harkokin noma da tattalin arziki baki daya dabaibayi da karfen-kafa.
Ya ce yi lambu a gida abu ne da ake girbar albarkar noman sa da wuri, kuma a dace ana cin moriyar sa.
Ya ce wannan tsarin lambu harka ce mai sauki ta hanyar amfani da iska, hasken rana da kuma ruwa domin a samar da abinci da muhalli a saukake.
Ya ce wannan hikimar lambu ba ta bukatar tafkekiyar gona. A cikin gidan ka ko bayan gida, ko a kango za a iya shuka iri kala daban-daban kuma nau’uka daban-daban ka ci moriyar su.
Terungwa ya ce a saukake mutum zai iya noma alayyahu, tattasai, tumatir, attarugu, yalo da sauran nau’ukan kayan miya da kayan marmari.
Za a iya shuka zogale, mangwaro, kwakwa, gwaba, gwanda da sauran su day dama.
A karshe ya ce GEFSEP za ta bayar da horo ga jami’an da za su rika bi su na ilmantar da mutane dangane yadda ake wanna lambu da kuma bi su na yi musu sa-idon kulawa da rainon lambunan.
Discussion about this post