Ranar 18 Ga Mayu,2020, PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Hukumar Tara Kudaden Shiga (FIRS) ta nada daraktoci hudu ba bisa ka’idar dokar aiki ba. Sannan kuma ta yi wa wasu daraktoci 9 ritaya ba bisa ka’ida ba.
Kafin PREMIUM TIMES ta buga labarin, sai da aka tuntubi FIRS, ta yi bayani wanda ba gamsasshe ba. Kuma hukumar ta ce wai ba ta kauce ka’idoji da dokokin dauka aiki, nada mukamai ko cire wasu ba.
Bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin, sai FIRS ta rude, ta gigice, ta rasa zaune kuma ta rasa tsaye. Ta kwasar milyoyin kudaden talakawa ta na biyan gidajen jaridu ana buga wa hukumar tallolin bata-sunan PREMIUM TIMES.
Sai dai kuma duk wa wanann borin-kunya, hauragiya da da kokarin zubar wa wannan jarida mutunci, PREMIUM TIMES na nan kan bakan ta cewa mahukuntan FIRS sun kasa bada gamsasshiyar amsar laifin cin zalin din daraktoci 9 da suka cire. Kuma sun nada wasu hudu a bisa karkatacciyar hanya, ba kan ka’idar da ta dace ba.
Ga Tambayoyin PREMIUM TIMES 11 da Hukumar FIRS ta kasa amsawa:
1. Shin an bi ka’idar da Gwamnatin Tarayya ta ce abi wajen nada daraktoci?
PREMIUM TIMES ta gano cewa ba a bi ba. Kuma mu na nan a kan bakan mu cewa ba a bi ka’idar ba. An kauce wa Sashe na 2.22.
2. Shin FIRS ta san sharuddan daukar ma’aikatan kwantaragi a karkashin Tsarin aikin gwamnati?
E, ta sani, amma ta take sanin da ta yi, ta yi ra’ayin kan ta.
3. Shin Hukumar FIRS ta bi ka’idar nada daraktoci hudu da ta yi? Ko an gudanar da binciken tantance bangarorin da ke bukatar daukar daraktocin?
Hukumar FIRS ta ce duk ta yi. Amma PREMIUM TIMES ta gano duk karya ta ke yi. Domin ko tallata gurabun ba a yi ba, don kada wadanda suka cancanta su san za a dauki daraktoci a hukumar har su nema
4. Shin FIRS na sane da cewa nada sabbin daraktoci hudu da ta yi ya kauce da tsarin shiyyoyin da ya kamata a dauko daraktocin kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta gindaya?
E, ta na sane, amma ta sa kafa ta take sanin.
5. Shin FIRS ba ta san cewa Shugaban Hukumar da Manyan Shugabannin Bangarori takwas na hukumar duk daga shiyya daya suke ba?
Idan sun ce hakan ba nuna bangaranci ko tauye wasu shiyyoyi ba ne, ta ya za su kauce wa zargin sauran ‘yan bangaren Najeriya da ke zargin cewa tunda manyan Hukumar akasari ‘yan bangare days ne, za su iya shirya wata harkalla su binne ba tare da an sani ba?
6. Shin a bisa ka’ida FIRS ta yi wa wasu daraktoci ritaya kuwa?
FIRS dai ta ce kwarai. Amma PREMIUM TIMES ta gano cewa karya ta ke yi.
7. Shin kafin Hukumar Gudanarwar FIRS ta yi wa daraktocin nan 9 ritaya, an kuwa karanta dokar ritayar daraktoci ta 10.1 (a) (iii)?
E, hukumar ta na sane da dokokin, amma aka sa kafa aka tattake su.
8. Me ya sa Shugaban Hukumar FIRS ya ki bin umarnin takardar da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya aiko masa, dangane da matakai da sharuddan dakatar da daraktoci?
9. Shin Hukumar FIRS ta fi Babban Bankin Najeriya karfin ikon cin gashin kai ne?
Wasikar umarnin tsaida dakatar da daraktoci daga Ofishin Shugaban Kasa ya lissafa FIRS a jerin hukumomi ta 16.
Wannan ya nuna FIRS karya ta ke yi, ba cin gashin kan ta ta ke yi ba.
Discussion about this post