Mummunan tashin hankali ya faru a rugar Zuwo, cikin Karamar Hukumar Gubio a Jihar Barno.
Da rana tsaka ne a ranar Talata Boko Haram suka far wa makiyayan da ke rugar Zuwo takakkiya suka yi musu mummunan kisan da suka shafe mazan kauyen baki dayan su.
Wani dan sintiri ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram sun yi wa makiyaya maza da kananan yara kisan-kiyashi misalin 12 na rana, a inda suke taruwa su na kai shanun su su sha ruwa.
Mala Buni ya ce da idon sa ya gani, kuma ya kirga gawarwaki 69 ta mazaje da kuma kananan yara.
Sannan kuma ya ce akalla an arce da shanu sun fi 1,200. Kuma an kashe shanu za su kai 100.
“Wato harin kamar ramuwar gayya ce Boko Haram suka koma suka yi a cikin rugagen. Sun taba kai hari watanni biyu da suka gabata, amma makiyayan suka yi galaba a kan su, har aka kashe Boko Haram biyu.
Majiya ta shaida wa Premium Times cewa ‘yan Boko Haram sun sha kai samame a rugagen su na dora musu harajin-tilas. Wanda ya kasa biya sai a yi awon-gaba da dabbar sa.
“To da abin ya ishe su, sai suka fara nuna tirjiya har su na korar Boko Haram din.” Inji Mala.
Yadda Aka Yi Wa Makiyaya 69 Kisan-kiyashi:
“Akwai wata mashayar ruwa da gwamnati ta gina rijiyoyin burtsate domin shayar da dabbobin makiyaya.
“To a mashayar ruwa din ce Boko Haram suka ritsa makiyayan manya da kanana. Sun je cikin motar daukar sojoji budaddiyya har guda uku.
“Da suka fara bude wuta, makiyayan sun ja daga, amma da ya ke shammatar su aka yi, sai suka labewa jikin shanun su.
“Su kuma Boko Haram sai suka rika bude wuta kawai a kan shanun da masu boyewa a bayan shanun.
“An kashe mutum 69, Kuma an kashe shanu za su kai 100.” Cewar majiyar PREMIUM TIMES.
Bayan awa daya da faruwar lamarin, sojoji sun rika shawagi bisa jirgin yaki a wurin, amma dai ba su bi Boko Haram da harbi ba, duk kuwa da cewa ba su fi awa daya da barin wurin ba.
An ce sun sake komawa kauyen da yamma, suka kashe mutum daya da ya rage, wanda da farko ya tsere daga wurin kisan kiyashin a kan doki.
Bayan sun kashe shi, sun banka wa kauyen wuta kurmus.
Lokacin da ake rubuta wannan labarin ma kauyen na cin wuta.
Majiya ta ce tuni Gwamna Zulum ya garzaya kauyen.
Discussion about this post