A wani faifan bidiyo mai tsawon sakan 49, Boko Haram bangaren ISWAP sun nuna yadda suka kashe wani soja daya da Dan sanda daya da suka kama cikin makon da ya gabata.
Sun kama jami’an tsaron ne a kan hanyar su ta zuwa Monguno daga Maiduguri.
Cikin bidiyon an nuno kowanen su ya na gabatar da kan sa kafin a bindige su.
Dan Sanda: “Suna na Insifeto Yohanah Kilus. Sojojin TIlafa ne suka kama ni a hanyar Monguno.”
Kilus da Hausa ya yi bayanin gabatarwar sa.
Soja: “Ni ne Lance Kofur Emmanuel Oscar, mai lamba /3NA/70/8374. Sojojin Talifa suka kama ni a hanyar Monguno.
Daga nan sai aka nonu wani durkushe ya yi saitin su day bindiga. Ya bi su ya bindige.
Ba a dai san lokacin da aka bindige su ba. Amma dai an bindige su kwana uku bayan mummunan kisan mutum 81 da Boko Haram suka yi a Karamar Hukumar Gubio, jihar Barno.
Discussion about this post