Uwargidan marigayi Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo, Florence Ajimobi ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda gwamnatin jihar Oyo ta banzatar da mijinta tun yana da rai har zuwa lokacin da ya rasu.
Cikin fushi Florence ta ce abinda gwamnatin jihar Oyo ta yi yayi matukar bata mamaki da takaici.
” Tsakani da Allah ace wai mijina ne gwamnan da ya sauka wannan ya hau jiya-jiya, amma wai ya kwanta bashi da lafiya gwamnatin jihar bata iya koda ta waya ne su kira ni su tambayi halin da yake ciki ba a asibiti.
” Mutumin nan ya shekara takwas ya na mulkin jihar Oyo, ay dai ya cancanci a ce gwamnatin jihar ko wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati sun tattaki har asibiti ba ma ta waya ba sun gaishe mu.
” Ina so kowa ya sani, abinda gwamnatin Oyo suka yi Mana basu kyauta ba.
Idan ba manta ba sanata Abiola Ajimobi ya rasu a wani asibiti a jihar Legas, bayan fama da yayi da rashin lafiya na gajeran lokaci.
Kafin ya rasu Ajimobi ne sanatan da ke wakiltar Shiyyar jihar Oyo a majalisar dattawa.
An yi jana’izar sa da 12 na rana ne a Oke-Ado, dake ibadan.
Wadanda suka halarci jana’izar sun hada da Kunle Saani, Sheikh Muideen Bello, babban limamin masallacin Ibadan, Sheik Abubakri Abdulganiyu Agbotomokere da wasu manyan malamai.
Ya rasu ya bar matar sa Florence Ajimobi da kuma ya’ya biyar.
Daya daga cikin ‘ya’yan sa Idris Ajimobi ya auri diyar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, Fatima Ganduje.
Allah ya ji kan sa, Amin.