Ministan Tsaro Bashir Magashi ya bayyana cewa daya daga cikin manyan matsalolin tsaron kasar nan su ne rashin isassun sojoji da matsalar wadatar kudaden shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.
Magashi ya you wanna bayani a gaban manema labarai na Fadar Shugaban Kasa, ranar Laraba, Jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Muhammadu Buhari.
Magashi, wanda ya ce sun tattauna kalubalen da fannin tsaron kasar nan ke fuskanta, ya ce ya gabatar da cikakken bayanin irin nasaori da kalubalen da harkar tsaron kasar nan ke fuskanta, tare da bayyana rashin wadatattun kudade da rashin isassun sojoji.
“Mun gode Allah, domin an bayar da shawarwarari da dama, kuma bisa yadda aka tattauna a yau, nan ba da dadewa ba za a magance dukkan wadannan matsaloli.
Najeriya na fuskantar gagarimar matsalar Boko Haram, ta ‘yan bindiga da kuma ta barayin danyen man fetur.
A baya Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Tukur Buratai ya sha yin korafin cewa ba su samun kudaden da Gwamnatin Tarayya ke yi wa harkar tsaro kasafi.
Wannan korafi ya zo daidai lokacin da Najeriya ke ware makudan kudade wajen magance matsalar tsaro fiye da kasafin bangaren ilmi da na kiwon lafiya.
An ware wa fannin tsaro naira bilyan 878 a kasafin 2020 wanda ba a ma fara amfani da shi ba.
Sojojin Najeriya na cikin tsaka-mai-wuyar yake-yaken tabbatar da tsaro, wadanda yawanci ayyuka ne na ‘yan sanda aka jibga musu, saboda rashin wadatar ‘yan sanda da kasar ke fama.