TITIN ABUJA ZUWA KANO: An shimfida sabuwar kwalta tsawon kilomita 102, saura kilomita 274 – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa an fara cin karfin aikin shimfida sabuwar kwalta daga Abuja zuwa Kano.

A jawabin sa na sabuwar Ranar Dimokradiyya, watau 12 Ga Yuni, Buhari ya ce a yanzu haka aiki ya nausa, har an kammala tsawon kilomita 102 daga cikin kilomita 376 da ya ce za a karce a sake shimfidawa.

Aikin ginin titin dai kamfanin gine-,gine na J. Berger ne ke gudanar da shi, kuma an dade da fara shi.

PREMIUM TIMES HAUSA ta fahimci yadda matafiya kan titin ke yawan korafin afkuwar hadurra da asarar rayuka da dukiyoyi sanadiyyar tafiyar-hawainiyar da aikin ke yi, wanda jaridu da dama a farkon shekarar nan sun yi rahotanni a kan yanayin tafiyar aikin.

Sannan kuma wakilin mu ya tabbatar da cewa yanayin tafiyar aikin titin ya sa motoci na daukar tsawon lokaci daga Abuja kafin su karasa Kano.

Wakilin PREMIUM TIMES ya shaida cewa tafiyar Abuja zuwa Kano a can baya, ba ta kai awa biyar ba. Amma yanzu idan mota ta isa cikin awa bakwai, to ta isa da sauri kenan.

Baya ga aikin titin Abuja zuwa Kano, wasu karin ci gaba da Buhari ya sake bayyanawa sun hada da aikin gina titina a karkashin Tsarin Titinan Kudin SUKUK.

A wanann tsari Buhari ya ce tuni har an gina titina daban-daban, wadanda jimlar tsawon su ya kai kilomita 412, daga cikin kilomita 643 da gwamnatin sa ta kudirci shimfidawa a karkashin SUKUK.

Sannan kuma Buhari ya ce aikin Gadar Kogin Neja (River Niger), wadda ta hade Arewaci da Kudancin kasar nan, an ci karfin sa har an kammala kashi 48 bisa 100.

“Ita ma Hukumar Ayyukan Gyara da Kula da Titinan Gwamnatin Tarayya (FERMA) ta yi rawar gani. Domin ta yi facin titi jimla tsawon kilomita 4000 daga cikin kilomita 5000 da aka kudirci yi wa faci.

Da ya koma kan jiragen kasa kuwa, Buhari ya ce an damka aikin fara shimfida layin dogo daga Kano zuwa Maradi. Kuma an damka na Fatakwal zuwa Maiduguri, wanda zai keto har cikin jihar Gombe.

Da dama jama’a na korafin cewa a duk shekara sai dai a yi ta sheka wa Arewa ruwan alkawurra. Amma akasarin ayyukan da aka kammala duk a kudu su ke.

Buhari ya ce aikin titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan an kammala kashi 90% bisa 100%.

Sai dai kuma hakan na nuni da cewa ba a ma fara aikin jirgin kasa din daga Ibadan zuwa Kano ba.

Share.

game da Author