TATTAUNAWA: Mun bai wa Buhari shawara dangane da batun bude makarantu, masallatai da coci-coci – Boss Mustapha

0

Wannan ce tattaunawar mu da Shugaban Kwamitin Yaki da Coronavirus, Boss Mustapha, bayan da ‘yan kwamitin suka fito daga taron ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, a Fadar Villa.

MUSTAPHA: Abin da mu ka tattauna shi ne mun gabatar wa Shugaban Kasa rahoton mu na ci gaban da mu ka samu a wannan mako biyu na karin wa’adi. Mun kuma rubuta masa shawarwarin da ya tabbatar mana da cewa zai duba ya yi abin da ya dace.

Sannan kuma ya jinjina wa ma’aikatan mu wajen hobbasa da sadaukarwar su, musamman jami’an kiwon lafiya da jami’an tsaro.

Sannan kuma mun yi masa bayanin irin abin da mu ka cimma wajen aikin gwaji da kuma yanayin da jama’a ke nuna bin umarnin dokar yin kaffa-kaffa.

Shugaba Buhari ya hore mu mu ci gaba da nuna wa jama’a cewa wannan gagarimin aiki fa na su ne. Da hadin kan su za iya samun nasara. Su zage damtse su rika kiyaye kan su da kan su da kuma iyalan su baki daya.

TAMBAYA: Ya ake ciki game da jihohin Kogi da Cross River, wadanda suka ki bai wa NCDC hadin kai? Kun yi wa Buhari wannan maganar kuwa?

MUSTAPHA: Mun dai tattauna kalubalen da mu ke fuskanta baki daya. Kuma ina da tabbacin cewa jawabin da zai yi, zai tabo duk wata matsala da ake fuskanta.

Saboda na san cewa duk abin da ya shafi wata jiha ita daya, to zai iya fantsama a cikin sauran jihohi.

TAMBAYA: Wasu jihohi sun bude masallatai da coci-coci, bisa ikirarin cewa abin fa sai an rika hadawa da addu’a. To ko kum tattauna wannan da Shugaban Kasa?

MUSTAPHA: Kusan batun da mu ka bada shawara kenan dungurugum. Amma a yanzu dai umarnin sa kawai mu ke jira. Idan ya bada umarni, mu kuma za mu zartas da abin ya ce.

Ka san a yanzu an zo karshen kwanakin karin makonni biyu. Kuma an shiga mataki na biyu na yaki da cutar Coronavirus. Wato matakin cudanya da kamuwa a cikin jama’a. Mutane kuma su ne jama’a.

Jama’a kuma a cikin jihohi su ke da Kananan Hukumomi. Saboda haka wannan mataki na gaba da za a dauka, jihohi ne za su ja ragamar shirin said kananan hukimomi da shugabannin al’umma, irin su sarakunan gargajiya, malaman addinai da sauran su.

Abin lura, kashi 60 bisa 100 na wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan, a cikin kananan hukumomi 20 kacal aka same su. Kuma fa kananan hukumomi 774 mu ke da su a kasar nan. Ashe ka ga kenan a yanzu aiki zai karkata ce a cikin dandazon jama’a.

Mun gabatar da kudirin shawarwari ga Shugaban Kasa, kuma na tabbatar zai yanke shawara dangane da batun sake bude makarantu, masallatai da coci-coci da sauran irin su kasuwanni.

TAMBAYA: Idan mu ka kalli yadda a kullum ake kara samun yawan masu kamuwa da cutar Coronavirus, shin za ka iya cewa kun samu nasara kuwa?

MUSTAPHA: Za iya cewa mun yi nasara, idan ka kalli karancin yawan wadanda cutar ta kashe. Sannan ka duba ka gani, mun fara da cibiyoyin gwaji biyar kadai. Amma yanzu mu ba da 28. Masana da sauran kwararru za su ce maka Coronavirus za ta kama kashi 80 bisa 100. Amma kashi 20 ne kadai za su nuna alamun ta a jikin su. Sauran za su iya kamuwa, har su warke sarai, ba tare da ma ta nuna alamu a jikin su ba.

Saboda haka duk da cewa akwai yakinin yawan wadanda za su kamu nan gaba zai iya karuwa, duk da haka ba za mu yanzu kauna ko yarda guyawun mu su sare ba.

Share.

game da Author