Gwamnatin Amurka na bibiyar Sanata Buruji Kashamu na Najeriya domin ya gabatar da hujjojin masaniyar sa dangane da shirin kai harin 9 Ga Satumba, 2001 a Amurka.
Wasu ‘Yan Ta’adda ne dai su ka kai wa Amurka mummunan hari ta hanyar karkatar da jiragen fasinjojin da suke ciki, inda suka fada a Cibiyar Hada-hadar Kasuwanci ta Duniya (World Trade Centre), a New York.
An kuma kai a Hedikwatar Leken Asiri ta Pentagon da wasu wuraren da aka kashe sama da mutum 3,000. Wasu 25,000 kuma suka ji munanan raunuka.
Yadda Buruji Kashamu Ya San Za A Kai Harin 9/11
Kashamu ya ji masaniyar kulle-kullen kai hari a Amurka, a lokacin da ya ke tsare a wani gidan kurkuku da ke Brixton a England.
An kama shi a tsare ne a ranar 18 Ga Disamba, 1998, bayan an same shi ya shiga kasar dauke da dala 230,000. Kuma da fasfo din kasar Benin aka kama shi.
Watanni bakwai kafin wannan kamu kuwa, Amurka ta na neman sa ruwa a jallo, domin tuhumar sa da laifin fasa-kwaurin kwayar hodar Iblis a kasar.
Yayin da ya ke tsare a kurkukun Ingila, abubuwa biyu sun faru duk masu muhimmanci.
Na farko dai Amurka ta rika tayar da kayar-baya dole sai Ingila ta mika mata Buruji Kashamu domin ya amsa tuhumar shigar mata da hodar Iblis a kasa.
Na biyu kuma lokacin da ya ke a tsare, ya rubuta bayanan rantsuwar-kaffara-kotu (affidavit), cewa ya yi labarin shirin kai hari Amurka daga bakin wani dan ta’adda da ke tsare a kurkuku, kuma a daki daya suke tsare su biyu.
Kani na Adewale ne ya shiga da kwaya Amurka, ba ni ba – Buruji Kashamu
A kokarin da Kashamu ya yi domin kada Ingila ta auna shi zuwa Amurka ya fuskaci hukunci, lauyoyin sa sun shaida wa Mai Shari’a Thimothy W na Kotun Majistaren Brixton cewa dan uwan sa ne mai suna Adewale Kashamu ya taba yin safarar kwaya zuwa Amurka, ba shi Buruji din ba.
An tambayi Kashamu ina dan uwan nasa? Sai ya ce ai jami’an kwastan sun bindige shi cikin 1989, lokacin da ya yi wani kokarin shiga da kayan sumogal a Najeriya.
Rashin kwararan shaidu ya sa Mai Shari’a Thimothy ya ki tura Kashamu Amurka.
Karya Kashamu ke yi, shi ne Dillalin kwaya ba Adewale ba – Amurka
Ita kuwa Amurka, ta tsaya kai da fada cewa karya Kashamu ke yi ba shi ma da wani kani Adewale. Domin wasu mata abokan harkallar Kashamu da Amurka ta damke, wato Catherine da Ellen, sun ce Kashamu ne ogan safarar kwayar su. Kuma kowace ta nuna hoton ta, ta ce shi ne.
Sannan kuma an nemi Kashamu ya gabatar da hoton kanin na sa Adewale, amma abu ya faskara.
Kashamu: Daga Kwaya an koma batun harin 9/11
PREMIUM TIMES ta mallaki kwafe-kwafen dukkan bayanan da lauyan sa ya ce Kashamu ya rika yi wa jami’an tsaron Amurka da na Ingila dangane da harin 9/11.
Sannan kuma wannan jarida ta gano yadda Kashamu ya gulmata wa jami’an tsaron Amurka labarin cewa za a kai harin ranar 11 Ga Satumba din, amma jami’an tsaron ba su yi wani abu ba.
Dalla-Dalla:
1. Ranar 2 Ga Satumba, Kashamu ya rubuta takardar bayanan rantsuwar-kaffarar-kotu (affidavit) cewa, ya rantse da Allah ya ji daga bakin wani dan ta’adda da suke tsare a daki daya cewa za a kai hari a Amurka.
2. Lauyan Kashamu mai suna Thomas Darkin ne da ke ofishin Chicago Laws ya aiki wa jami’an tsaron Amurka wasikar, a madadin Kashamu.
3. Bayan sun karbi wasikar, ba su yi wani abu a kai ba, har sai bayan da aka kai harin.
Bayan an kai hari:
4. Wani lauyan gwamnatin Amurka mai suna Patrick Fitzgerald ya je har Ingila ya ya samu Kashamu a kurkuku ya yi masa tambayoyi.
5. Ranar 30 Ga Disamba, 2001, jami’an ‘yan sandan Ingila (Scotland Yard), da ke karkashin ‘Yan Sandan Birni Da Kewaye (Metropolitan Police), sun je har kurkuku sun yi wa Kashamu tambayoyi.
6. Tambayoyin farko da aka yi masa, ya bayar da bayani a rubuce tsawon shafukan takarda 3.
7. Can baya a ranar 6 Ga Nuwamba, ya yi rubutaccen bayani mai shafuka bakwai.
8. Tun a ranar 21 Ga Satumba, mako biyu bayan kai hari, Fitzgerald ya rubuta wa Kashamu ta hannun lauyan sa Durkin cewa duk abin da ya yi bayani ba za a yi amfani da shi a kotu wajen hukunta shi ba.
9. Kashamu ya ce Kotun Amurka sa ke Gundumar Arewacin Illinois ta nemi Kashamu ya amsa laifin shiga da kwaya, domin a yi masa sasaauci. Amma shi ya ce ba zai amsa laifin da bai aikata ta ba.
10. Cikin 2015, Amurka ta nemi Najeriya ta aika mata da Kashamu, amma wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta hana.
11. Sake bibiyar batun karin bayanin harin 9/11 da Amurka ta yi daga bakin Kashamu, ya nuna har yau ba ta hakura da shi ba.